PDP ta kafa kwamitin kamfen din Atiku

PDP ta kafa kwamitin kamfen din Atiku

Jam'iyyar adawa ta PDP ta rantsar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa karkashin jagorancin shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, yau, Alhamis a Abuja.

Za mu kawo ma ku karin bayani a kan wannan rahoto....

A wani rahoton Legit.ng mai nasaba da wannan, kun ji cewar dan takarar shugabacin kasa na jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP, Atiku Abubakar ya ce bashi da wata tantama a zuciyarsa cewa jam'iyyar PDP ce za ta lashe zabukkan 2019.

Atiku ya fadi hakan ne a yayin taron majalisar zartarwa na jam'iyyar da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce duba da yadda al'umma suka karkata zuwa jam'iyyar saboda adalcin da akayi a zaben fidda gwani na jam'iyyar da yadda 'yan takarar suka hade waje guda suna aiki, ya gamsu cewa jam'iyyar za tayi nasara a zabujan shekarar 2019.

PDP ta kafa kwamitin kamfen din Atiku

Atiku
Source: UGC

Atiku ya ce ya yi mamakin yadda shugbanin jam'iyyar suka gayyaci shi suka bayyana masa adadin kudaden da jam'iyyar ta samu yayin gudanar da zabukkan cikin gida, ya ce bai taba ganin hakan a baya ba.

"Na ce mune za muyi nasara kuma ya zama dole mu lashe zaben shugabancin kasa, zamu kafa tarihi a matsayin gwamnatin wadda tafi rike amanar dukiyar yan Najeriya saboda haka shugabanin jam'iyyar mu suka koyar da mu, na jinjinawa ciyaman din jam'iyyar.

DUBA WANNAN: Abu biyu kacal gwamnatin Buhari ta samar - PDP

"Na yi imanin cewa da hadin kan dukkan ku, musamman gwamnoni da 'yan majalissun tarayya, shugabanin jam'iyya na dukkan matakai da magoya bayan mu, ina tabbatar muku cewa mu za muyi nasara a zaben.

"Mun taso da karfin mu tun bayan taron kasa da mu kayi a Port Harcourt, yanzu lokaci ne da ya kamata mu cigaba da gwagwarmaya har sai sun dira a Aso Villa." inji Atiku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel