Cin kudin SEC: An sake sa ranar da za'a ji Gwarzo na zai kare kansa

Cin kudin SEC: An sake sa ranar da za'a ji Gwarzo na zai kare kansa

- Kuto ta dage saurarar karar da SEC ta shigar zuwa 30 ga watan Junairu

- An bukaci su gabatar da shaidunsu a ranar da kotun zata sake zama

- An dakatar da Gwarzo tun a watan Nuwamba 2017 akan zargin sa da karkatar da wasu kudade

Cin kudin SEC: An sake sa ranar da za'a ji Gwarzo na zai kare kansa
Cin kudin SEC: An sake sa ranar da za'a ji Gwarzo na zai kare kansa
Asali: Twitter

Wata kotun ma'aikata dake Abuja ta dage saurarar karar da SEC ta shigar zuwa 30 ga watan Junairun 2019.

Kotun ta bada umarnin dakatar da darakta janar na SEC Mounir Gwarzo.

A yayin sake zaman kotun mai kare Gwarzo Adetayo Adeyemi ya gabatar wa da kotu wasu shaidu guda Uku.

DUBA WANNAN: Illolin tserewar da likitocin Najeriya sukeyi zuwa kasashen waje

Mai shari'a Sanusi Kado ya baiwa kowanne a cikin su damar bayyana abinda ke gareshi.

Kuto ta bada umarnin dakatar da Gwarzo ne tun a watan Nuwamba na shekara ta 2017 a bisa tuhumar sa da akeyi da karkatar da wasu kudade.

Sannan ya nemi kotun data bada umarnin biyan shi albashin sa tun daga ranar da aka dakatar dashi zuwa yanzu.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel