Alhazai 5 na Jihar Zamfara sun rasa rayukansu a Kasa mai Tsarki
Za ku ji cewa Hukumar jin dadin Alhazai reshen jihar Zamfara, ta bayyana cewa rayukan Alhazanta biyar ne suka salwanta yayin sauke faralinsu na aikin hajjin da ya gabata na wannan shekara 2018 a kasa mai tsarki.
Shugaban hukumar Alhaji Abubakar S-Pawa, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Gusau a yau Laraba dangane da sakamakon aikin hajji na 2018.
A cewarsa, cikin wadanda ajali ya katsewa hanzari sun hadar da shugabannin jam'iyyar APC na kananan hukumomin Maru, Kauran Namoda da kuma Shinkafi.
Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugabannin jam'iyyar sun rasa rayukan su a wani hatsarin Mota yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga birnin Makkah zuwa na Madina.
Sauran rayukan Mutanen biyu da suka salwanta sun hadar da Ayuba Azare da kuma Fadimatu Sani Makaranta da suka fito daga shiyyar karamar hukumar Gusau yayin da ajali ya katse ma su hanzari bayan wata 'yar gajewuwar rashin lafiya.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, baya ga mutane biyar da suka rasa rayukansu, Alhazai 2, 168 na jihar Zamfara sun dawo cikin koshin lafiya bayan amsa kiran Mai Duka a kasa mai Tsarki.
KARANTA KUMA: Hukumar Sojin Ruwa ta cafke 'yan Kasar Kamaru 6 da Sumoga ta Shinkafa a jihar Cross River
Kazalika gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagoranci Gwamna Abdulaziz Abubakar Yari, ta yabawa Alhazanta dangane da halayyar kirki ta mutane na gari da suka nuna yayin gudanar da Ibadunsu na sauke farali a kasar Saudiyya.
Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar jin dadin Alhazai reshen jihar Bauchi, ta fara shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji na 2019 kamar yadda babban sakataren hukumar, Alhaji Abdullahi Magaji Hardawa ya bayyana.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng