Duniya tayi Allah-wadai da Saudiya bayan da ta dawo da littafan zafafa ra'ayi a makarantun ta

Duniya tayi Allah-wadai da Saudiya bayan da ta dawo da littafan zafafa ra'ayi a makarantun ta

- Tarayyar Turai ta kushe koyarda kiyayya da rashin zaman lafiya da Saudi Arabia take koyawa dalibai

- Duniya ta duba litattafan makarantar masarautar ne daga 2017 zuwa wannan shekarar

- Litattafan sun kunshi wasu shafuka da aka cire a da amma aka dawo dasu

Duniya tayi Allah-wadai da Saudiya bayan da ta dawo da littafan zafafa ra'ayi a makarantun ta

Duniya tayi Allah-wadai da Saudiya bayan da ta dawo da littafan zafafa ra'ayi a makarantun ta
Source: UGC

Ofishin Amurka mai kula da harkokin masu addinai a kasashen duniya ya kushe masarautar Saudi Arabia saboda dawo da littatafai da tayi masu koyar da kiyayya da rashin zaman lafiya ga dalibai, wanda ke jefa su ta'addanci.

Hakan na kunshe ne a litattafan karatun su. Litattafai da aka fiye jin mujahidai na yanko wa da sunan suna aikin Allah.

Ofishin, mai suna USCIRF, ya ruwaito cewa an duba litattafan masarautar ne daga 2017 zuwa wannan shekarar inda aka gano shafuka da yawa da aka cire a da an maida su.

DUBA WANNAN: Masu kwakwalwa suna barin Najeriya duk mako

"Kara bayyanar shafukan ya sama sanadin tambayoyi da yawa akan cewa ko kasar Saudi Arabia tana gyara mai ma'ana ne a tsarin karatun ta," inji shugaban hukumar, Tenzin Dorjee.

Abin tsoro ma shine yadda wadannan koyarwar suke samun hanyoyin zagaye duniya a makarantun da Saudiyyar take tallafawa, sannan abun amfani ga kungiyoyin tsaurara addini irin su ISIS.

Ko Boko Haram ta Najeriya, da irin manhajar Saudiyya ta Wahabiyyanci mai saurin kafurtawa da son kashe mutane take aiki. Wanda hakan ya sanya dole suka koma daji da zama saboda basu iya jituwa da sauran jama'a.

Litattafan karatun an ruwaito cewa suna karfafa gwiwa akan jihadi ga wadanda basu yarda da musulunci ba tare kuma da yanke hukuncin kisa ga mata masu zina ko madigo, ko soyayya da junansu.

Wasu shafukan ma na magana akan tsaurara hukunci ga wadanda suka kalubalanci addinin musulunci.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel