Tiyata cikin buguwa: Likita ya kashe mai Jego da jaririnta

Tiyata cikin buguwa: Likita ya kashe mai Jego da jaririnta

- Wani likita mai shekaru 50, P.J Lakhani ya yiwa mai nakuda tiyata a yayin da ya ke buge da giya

- Jaririyar da aka cire ta mutu sannan daga bisani mahaifiyar ita ma ta mutu bayan zubda jini sosai

- Tuni dai yan sanda sun kama likitan kuma an fara gudanar da bincike domin gano idan sakacinsa ne ya yi sanadiyar mutuwan uwa da diyarta

An kama wani likita a garin Gujarat bisa zarginsa da yin tiyata a yayin da yake cikin mayen giya wadda hakan ya yi sanadiyar mutuwar jariri da mahaifiyarta a ranar Talata kamar yadda 'yan sanda suka sanar.

A cewar yan sandan, an kai mai nakudar, Kaminiben Chanchiya asibitin Sonawala a daren Litinin tana cikin nakuda yayin da likitan Dr. P.J Lakhani ya yi mata tiyata.

Jaririyar mace da aka haifa ta mutu sannan daga bisani Chanchiya itama da mutu wadda hakan ya sanya 'yan uwanta suka zargi likitan da sakaci, inji sufuritandan 'yan sanda, Harshad Mehta.

Tiyata cikin buguwa: Likita ya kashe mai Jego da jaririnta

Tiyata cikin buguwa: Likita ya kashe mai Jego da jaririnta
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Badakalar N29bn: Yadda wasu shaidu a tuhumar Nyako su ka yi mutuwar ban mamaki

"Yan sandan sun gano cewa likitan yana buge da giya ne lokacin da ya k bakin aiki a ranar. Tuni aka kama shi kuma aka dauki jininsa domin aikewa dashi wajen gwaji," inji Mehta.

Asibitin dai ya kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan dalilan mutuwar mai jegon da kuma dan na ta domin ganin idan mutuwarta yana da alaka da sakacin aiki ne ko kuma wasu dalilan daban ne suka yi sanadin mutuwar.

'Yan sanda sun shaidawa BBC cewa likitan mai shekaru 50 ne ya kira 'yan sanda da kansa ya nemi su taimake shi saboda yana tsoron iyalan marigayiyar suna iya kai masa hari idan suka gano cewa a buge ya yiwa 'yar uwarsu tiyata.

Wani abu mai kama da wannan ya taba faruwa a garin Ahmedabad a jihar Gujarat inda wanda yarinyar mai shekaru 2 ta rasu yayin da likita ke kula da ita alhalin yana buge da giya.

Likitan mai suna Jayant Patel ya yi ikirarin cewa rashin lafiyar yarinyar ya tsananta ne yayin da ake yi mata magana saboda haka mutuwarta ba shi da alaka da shan giyarsa kamar yadda Times Now ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel