Ba sani ba sabo: EFCC ta maka dan sarkin Zazzau gaban kotu akan wawuran naira miliyan 16

Ba sani ba sabo: EFCC ta maka dan sarkin Zazzau gaban kotu akan wawuran naira miliyan 16

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da yaron sarkin Zazzau, wanda shine hakimin Unguwar Mua’azu kuma Cika-Soron Zazzau, Aliyu Shehu Idris gaban babbar kotun jahar Kaduna kan zarginsa da zamba cikin aminci.

A ranar Talata 27 ga watan Nuwamba ne aka gudanar da zaman fara sauraron karar a gaban Alkalin kotun mai sharia Darisu Khobi inda EFCC ke tuhumar yariman da laifi guda daya tak wanda ya shafi zamba cikin aminci, inji rahoton Daily Nigerian.

KU KARANTA; Bani na baiwa EFCC kyautan naira miliyan goma ba – Gwamna Ganduje

Ba sani ba sabo: EFCC ta maka dan sarkin Zazzau akan wawuran naira miliyan 16
Cika soro
Source: Facebook

Ana tuhuman hakimin ne da damfarar wani Alhaji mai suna Yusuf Baban a shekarar 2012, inda ya hakimin ya sayar ma Yusuf da wani fili dake kan babbar titin data ratsa unguwar Muazu ta Nnamdi Azikwe Express Bye Pass akan kudi naira miliyan goma sha biyar da dubu dari tara.

Sai dai ashe duk wannan cinikin da aka yi ba da sani ko izinin asalin mai filin aka yi ba, wanda ake kira da suna Shuaibu Kazaure, don haka kararar ta tabbata zamba cikin aminci yariman zazzau yayi ma Alhaji Yusuf Baban.

Majiyar Legit.com ta ruwaito Alhaji Yusuf ya shaida ma kotu cewa Hakimin da kansa ne yayi masa tallar filin, amma ya bayyana masa cewa za’a iya sayar da filin ne kadai akan makudan kudade da suka kai naira miliyan goma sha bakwai, inda a ciki ya biya miliyan 15 da dubu dari 900.

Yusuf ya cigaba da fadin bayan an kammala cinikin sayan filin, an kuma rubuta takardar yarjejeniya a tsakanin mai saya da sayarwa, inda kowa ya gamsu da cinikayyar, sai dai a lokacin da Yusuf ya nemi hakimin ya bashi takardun filin, anan ne ido ya raina fata.

Yusuf yace yayi ta bin hakimin game da takardun filin, amma gogan naku ya hanashi, sai dai labarai da yake bashi iri iri daban daban na tsawon lokaci, daga nan ne ya fara tunanin akwai lauje cikin nadi, amma fa ba zata sabu ba.

“Da na gaji da bin takardun filin, sai na nemi ya bani kudin dana biya, na fasa cinkin, amma ya hanani, daga nan ne na yanke shawarar kai kara ga EFCC.” Inji shi. Sai dai hakimin ya musanta tuhumar gaba daya, inda yace bai san anyi ba.

Daga nan sai lauyan hakimin ya nemi a bada belin wanda yake karewa, sai Alkali ya amince da bukatarsa, ya bada belin hakimin akan kudi naira miliyan daya da mutum guda da zai tsaya masa akan naira miliyan daya, sa’annan ya dage sauraron karar zuwa 14 ga watan Janairun 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel