Shugaba Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Abba Kyari

Shugaba Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Abba Kyari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa da mutuwar tsohon gwamnan jahar Arewa ta tsakiya, wanda ta koma Kaduna, Birgediya Abba Kyari, wanda ya rasu a daren Lahadi, 25 ga watan Nuwamba kamar yadda Legit.com ta ruwaito.

Buhari ya bayyana ta’ziyyar mutuwar Abb Kyari ne ta bakin babban hadiminsa akan harkokin watsa labaru, Garba Shehu, wanda ya bayyana marigayin a matsayin wani babban mutumi da Buhari ke ganin kimarsa.

KU KARANTA; Innalillahi wa inna ilaihi rajiun: Tsohon gwamnan Kaduna Abba Kyari ya rasu

Shugaba Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Abba Kyari
Abba Kyari
Asali: Facebook

Haka zalika shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta ma al’ummar jahar Kaduna da Katsina, jihohin da Abba Kyari ya mulka a matsayin gwamna, da ma al’ummar jahar Borno, cibiyar marigayin da gwamnatocin jihohin gaba daya bisa wannan babban rashi da suka tafka.

“Mun kadu matuka da mutuwar Janar Abba Kyari, gogaggen hafsan Soja, kuma mutumin kirki mai mutunci a idanunmu, ina fata Allah ya jikansa da gafara, kuma ya baiwa iyalansa hakurin rashi. Amin.” Inji Buhari

Legit.com ta ruwaito wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, kuma Da ga mamacin, Mohammed Kyari ne ya tabbatar da mutuwar mahaifin nasa ta shafinsa na Facebook, inda yace babansu ya mutu ne bayan doguwar jinya.

Shugaba Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Abba Kyari
Abba Kyari
Asali: UGC

Shi dai Abba Kyari ya zama gwamnan Arewa ta tsakiya ne a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, janar Yakubu Gowon, daga ranar 28 ga watan Mayu zuwa watan Yuli na shekarar 1975.

A shekarar 1967 ne janar Yakubu Gowon ya samar da jihohi goma sha biyu a Najeriya bayan ya rushe shiyyoyin Arewa da na Kudancin Najeriya, inda a cikin shiyya Arewa kadai sai daya samar da jihohi guda shida, daga cikinsu akwai jahar Arewa ta tsakiya, wanda daga bisani aka canja mata suna zuwa Kaduna a shekarar 1976.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel