2019: Gwamnoni da 'yan majalisar APC a jihohin arewa 6 sun yi taro a kan Atiku

2019: Gwamnoni da 'yan majalisar APC a jihohin arewa 6 sun yi taro a kan Atiku

Shugabannin jam'iyyar APC da suka hada da gwamnoni da 'yan majalisar tarayya daga yankin arewa maso gabas sun yi wani muhimmin taro yau, Lahadi, domin tattauna yadda za su bullowa dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Jam'iyyar APC na da gwamnoni 4 daga cikin 6 da yankin ke da su. Sai dai babban kalubale da APC kan iya fuskanta shine batun cewar Atiku ya fito ne daga yankin na arewa maso gabas.

Shugabannin APC a yankin sun ce alhakin kayar da Atiku a yankin ya rataya a wuyansu.

Duk da kasancewar Atiku ya sha yin takara a baya ba tare da tabuka wata rawar gani ba a yankin, ma su nazarin siyasa na ganin cewar wannan karon za a fafata da shi saboda karfin jam'iyyar da yake takara a cikinta da kuma karfin arzikin da yake da shi.

Wannnan shine karo na farko da Atiku ya samu damar yin takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP tun bayan lashe zaben gwamna da ya yi a jam'iyyar a shekarar 1999, kafin daga bisani Obasanjo ya zabe shi a matsayin mataimaki.

2019: Gwamnoni da 'yan majalisar APC a jihohin arewa 6 sun yi taro a kan Atiku
Wasu Gwamnoni APC a wurin tantance a 'yan takara
Asali: UGC

Da yake magana yayin taron na shugabannin na APC a yau, Kashim Shettima, gwamnan jihar Borno, ya ce takarar Atiku ba zata hana Buhari samun nasara a yankin ba.

"Yankin arewa maso gabas na Buhari ne; shine dan siyasa mafi farinjini a yankin kuma da yardar Allah zai kara samun nasara a zaben 2019 a yankin arewa maso gabas.

DUBA WANNAN: 'Yan kasuwar shanu 15 daga arewa sun mutu a hanyar su ta kai dabbobi kudu

"Muna yiwa dan takarar jam'iyyar PDP fatan alheri, amma muna son yiwa jama'a tunin cewar ita siyasa da yawan jama'a ta ke aiki kuma shugaba Buhari ne keda rinjayen jama'ar yankin arewa maso gabas.

"Tabbas shugaban Buhari zai kara samun kuri'un jama'ar yankin arewa maso gabas domin tarihi ne zai maimaita kansa."

Ragowar gwamnoni da 'yan majalisa da su ka halarci taron sun bayyana cewar shugaba Buhari ne zai lashe mafi rinjayen kuri'un yankin a zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng