Gwamnati zata kasa biyan N30,000 saboda farashin mai yayi qasa
- Faduwar farashin mai zai iya zama barazana ga tattalin arzikin kasa
- Farashin mai ya fadi da kashi 6.1 a ranar juma'a wanda hakan ya kai shi dala 50.42
- Hakan zai iya shafar kasafin kudin shekarar 2018 wanda aka kayyade da dala 51 duk ganga
Faduwar farashin danyen man fetur zai iya kawo nakasu ga tattalin arzikin kasa, inji masu ittifaki a harkar mai da iskar gas.
Farashin danyen man ya fadi a ranar juma'a inda man Brent ya fadi da kashi 6.1 wanda yanzu ganga daya dala 58.80. Shi kuma WTI ya fadi da dala 4.21 inda ya kai dala 50.42 ganga daya.
A wannan cigaban, tabbatar da kasafin kudin Najeriya na 2018 zai iya samun tangarda in har faduwar ta cigaba, inji tsohon shugaban kungiyar tattalin arzikin wuta na Najeriya, Farfesa Adeola Adenikinju, wanda ya sanar da majiyar mu.
DUBA WANNAN: Yawan yara da basu zuwa makaranta a Najeriya
Faduwar farashin man fetur din ta biyo baya ne sakamakon samun danyen man da yawa bayan hadin kai tsakanin masu samar da man.
Masana a a harkar tattalin arzikin sun nuna damuwar su akan yanda da farko tattalin arzikin Najeriya ya fara daidaituwa da man fetur wanda faduwar shi zata iya kawo sanadin faduwar tattalin arzikin kasar.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng