Kotu ta yankewa mamba a majalisar dokokin jihar Zamfara hukuncin daurin shekaru 4

Kotu ta yankewa mamba a majalisar dokokin jihar Zamfara hukuncin daurin shekaru 4

Wata babbar kotun jihar Zamfara dake zamanta a garin Gusau ta yankewa Lawali Attahiru Dogonkade, mamba a majalisar dokokin jihar Zamfara, daurin shekaru 4 a gidan yari bayan samun sa da laifin damfarar N31m.

Alkalin kotun, Jastis Bello Shinkafi, ya yankewa Dogonkade wannan hukunci ne a ranar Juma'a bayan hukumar ICPC ta gurfanar da dan majalisar.

Hukumar ICPC ta gurfanar da Dogonkade ne a kan tuhuma guda 4 ma su nasaba da damfara. Dogonkade ya amsa laifin da ake tuhumar sa da aikatawa.

Har ya zuwa lokacin da aka yanke masa wannan hukunci, Dogonkade ya kasance dan majalisar dokokin jihar Zamfara dake wakiltar mazabar Kauran-Namoda.

Dan majalisar ya yi amfani da matsayinsa wajen yin zambatar kudin sayen kayan aiki a asibitoci na fiye da miliyan N31m. Laifin da ya saba da sashe na 10, 12 da 19 na kundin hukumar ICPC da aka kirkira a shekarar 2000.

Kotu ta yankewa mamba a majalisar dokokin jihar Zamfara hukuncin daurin shekaru 4
Dogonkade
Asali: Depositphotos

Lauyan hukumar ICPC ya shaidawa kotu cewar Dogonkade ya karbi miliyan N4.5m daga hannun Mista Hamisu Saminu Jibril, shugaban kamfanin Madaci dake sayar da magunguna da kayan asibiti a matsayin kudin ladan kwangilar da gwamnatin jihar Zamfara ta ba shi.

DUBA WANNAN: Tsohon ministan PDP ya karbi kadarorinsa daga hannun EFCC bayan ya koma APC

Sai dai Abubakar Junaidu, lauyan da ke kare Dogonkade, ya nemi kotu ta yi sassauci a hukuncin da zata yankewa wanda yake karewa bisa hujjar cewar wannan shine karo na farko da aka samun shi da wani laifi makamancin wannan.

Biyo bayan wannan roko ne sai kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 4 a gidan yari ko kuma zabin biyan tarar N30,00 a kan kowacce daga cikin tuhuma hudu da ake yi masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel