Yara 14m ne basu zuwa makaranta a sabuwar qididdigar gwamnati

Yara 14m ne basu zuwa makaranta a sabuwar qididdigar gwamnati

- Gwamnatin tarayya ta Gaza ciyar da yan makarantar jihohi 10

- Wannan na daga cikin alkawarin da tayi yayin yakin neman zabe a 2015

- Duk da haka, tsarin ya samarwa da yan kasa aikin yi

Yara 14m ne basu zuwa makaranta a sabuwar qididdigar gwamnati
Yara 14m ne basu zuwa makaranta a sabuwar qididdigar gwamnati
Asali: Depositphotos

Kasawar Gwamnatin tarayya na samar da Naira biliyan 336 duk shekara yake kawo kasawar shirin ciyar da yan makaranta, hakan ne dalilin da yasa baa ciyar da sama da yaran makaranta miliyan 14 wanda jam'iyyar APC ta alkawari kafin hawa mulki.

Idan aka tabbatar da ciyar da yaran yanda ya dace, yan makaranta miliyan 24 ne zasu amfana da hakan a fadin kasar.

DUBA WANNAN: Faransa zata dawo wa da Afirka arzikinta

A yanzu, duk da an dauki masu girki 97,000, manoma 150,000 don samar da abincin ciyar da yan makarantar wanda hakan ya samar wa mutane da yawa aikin yi.

Watanni Shida kacal suka rage wa mulkin, amma har yanzu jihohi 10 basu amfana daga ciyarwar ba. Daga Naira biliyan 336 na ciyar da yara miliyan 24 na makarantun gwamnati, Naira biliyan 651 ce kacal ta fito wacce take iya ciyar da yara miliyan 9.3 a jihohi 26 a duk shekara daya.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel