Sabon Labari: Za kuma a baiwa 'yan Road Safety makamai

Sabon Labari: Za kuma a baiwa 'yan Road Safety makamai

- Gwamnatin tarayya tana tunanin amincewa da bawa hukumar FRSC damar rike makamai

- Hukumar tana fatan za'a amince da wannan bukata

- Mai magana da yawun hukumar yace ba wani abu bane dan an basu wannan dama tunda sun daura damarar yaki ga masu take doka

Sabon Labari: Za kuma a baiwa 'yan Road Safety makamai
Sabon Labari: Za kuma a baiwa 'yan Road Safety makamai
Source: Depositphotos

Gwamnatin tarayya tace zata duba yiyuwar amincewa da baiwa hukumar nan ta FRSC damar rike makamai.

Hukumar tana bukatar a bata wannan dama inda har ta tanaji wajen ajjiye makaman nata a wani waje a jihar Abuja.

Mai magana da yawun hukumar yace ba wani abu bane dan an basu wannan dama tunda sun daura damarar yaki ga masu take doka

DUBA WANNAN: Soji sun kama qasurgumin dan fashin nan da ya addabi kurmin Najeriya

Mai magana da yawun hukumar Bisi Kazeem yace ba wani abun tur bane idan an amincewa hukumar daukar makamai duba da cewa sun daura damarar yaki ga masu son karya doka.

A shekara ta 2016 ma'aikatan hukumar sun rasa rayukan su a dalilin yan fashi ko kuma diribobin dakeson gujewa ma'aikatan.

Wanda wannan ya sanya hukumar take tunanin nemawa ma'aikatan ta kariya.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng