Zan yi ritaya daga Siyasa a 2023 - Sanata Orji
Tsohon gwamna kuma Sanata mai ci da ke wakiltar jihar Abia ta Tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Theodore Ahamefule Orji, ya bayyana cewa zai yi hannun riga da siyasa a shekarar 2023 muddin yayin nasara a zaben 2019.
Orji ya bayyana cewa duk da kasancewar abu ne mai wahala ga 'yan siyasa su raba gari da ita, zai yi kokarin yin fice a wannan lamari da sauran 'yan siyasa za su yi koyi tare da bibiyar sahu irin na sa.
Ya ke cewa, zai yi ritaya daga harkokin siyasa da ba zai sake neman takarar wata ba kujera ba bayan shekarar 2023. Sai dai zai kasance tamkar wani madubin dubawa kuma mashawarci a harkokin siyasa sakamakon dadewa da kuma gogewarsa a cikin ta.
Sanata Orji ya yabawa gwamnan jihar kuma magajin kujerarsa, Gwamna Okezie Ikpeazu, inda ya jinjina ma sa ta fuskar kwazo da a halin yanzu ya ke sa ran da kyautata gami goyan bayan sa na sake lashe kujerar sa a zaben 2019.
Tarihi ya bayyana cewa, Sanata Orji ya jagorancin gwamnatin jihar Abia na tsawon wa'adin shugabanci biyu da dokar kasa ta ba shi dama bayan lashe zaben kujerar gwamnan jihar a shekarar 2007 kuma ya maimata a zaben 2011.
KARANTA KUMA: Wutar Gobara ta lashe babbar Kasuwa a jihar Katsina
Ko shakka ba bu jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, Sanata Orji ya ci gajiyar wannan kujerar a hannun tsohon gwamnan jihar, Orji Uzor Kalu bayan ya kasance shugaban ma'aikata na gwamnatin sa.
Kazalika jaridar ta kuma ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar, ya shawarci al'ummar kasar nan kan tabbatar da tumbuke duk wani shugaba a zaben 2019 da bai tabuka komai a kan karagarsa ta kujerar mulki.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng