Magu ya garzaya Ingila neman a dawo da Diezani
Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC), Ibrahim Magu, ya isa kasar Ingila a yunkurin a hukumar sa na son ganin n dawo da tsohuwar ministar man fetur, Diezani Allison Madueke, da ragowar 'yan Najeriya da ke zaman gudun fuskantar shari'a a Najeriya.
Bayan neman dawo da Diezani, Magu na neman a a dawowa da Najeriya kudaden da aka sata aka jibge a kasar.
A jiya, Alhamis, ne Magu ya gana da shugaban hukumar binciken laifuka na kasar Ingila (NCA) domin tattauna kokarin EFCC na ganin an dawowa da Najeriya kudade da kadarorin da aka boye a kasar.
DUBA WANNAN: An kashe kuku bisa zarginsa da sata a gidan gwamna Dankwambo
Yayin ganawar, Magu ya yiwa jami'an gwamnatin kasar Ingila bayanin dalilin EFCC na son a mayar da tuhumar Diezani Najeriya.
Wannnan bayani na kunshe ne cikin wani jawabi da mukaddashin kakakin hukumar EFCC, Tony Orilade, ya fitar.
Sanarwar ta kara da cewa Magu da jami'an NCA sun tattauna yadda za gaggauta mayar da tuhumar Diezani zuwa Najeriya tare da sanar da cewar Magu ya gamsar da jami'an dalilin EFCC na son gurfanar da Diezani a Najeriya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng