Kungiyoyin Arewa ba sa da nasani kan juyawa Jonathan baya a 2015
Kungiyar shawarwari ta Arewa watau Arewa Consultative Forum, ACF, da kuma kungiyar Dattawan Arewa ta Northern Elders' Forum, NEF, a jiya Laraba sun sake jaddada matsayarsu ta rashin da nasanin nuna adawa ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan.
Kungiyoyin biyu sun yi tarayya da juna cikin bayyana rashin da nasani kan tsagwaran adawa da suka nuna da kuma juya baya ga tsohon shugaban kasa yayin zabukan shugaban kasa da suka gudana a shekarar 2011 da kuma 2015.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, kungiyoyi biyun yayin ganawa da manema labarai na jaridar The Punch sun yi mursisi dangane da rashin nadamarsu tare da fayyace dalilai na juya baya ga tsohon shugaban kasa Jonathan yayin manyan zabukan kasa da gabata a baya.
Daga bangaren kungiyar ta ACF, ta bayyana cewa ya kamata shuwagabanni su rika sanin martaba da kuma girmama duk wani alkawali ko yarjejeniya da suka kulla tare da kare mutunci da tabbatar da gaskiya ta kalamansu.
Kakakin kungiyar dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi yayin ganawarsa da manema labarai ta hanyar wayar tarho ya bayyana cewa, yankin Arewacin Najeriya ya juya baya ga tsohon shugaban kasa Jonathan a sakamakon warware alkawalin siyasa na mallakawa tare da raba jagorancin kasar nan a tsakanin Kudu da Arewa karo bayan karo.
KARANTA KUMA: Secondus, Atiku da Gwamnonin PDP sun gana kan shirye-shiryen Zaben 2019 a garin Abuja
Farfesa Ango ya ci gaba da cewa, kungiyar ko kadan ba ta sanya hijabi ko sirranta wannan adawa ba da ko shakka ba bu tsohon shugaban kasa Jonathan na da cikakkiyar masaniya ta dalilin ta.
Tsohon shugaban kasa Jonathan cikin wallafar sabon littafinsa da ya kaddamar a ranar Talatar da ta gabata ya bayyana cewa, ya fuskanci matsananciyar adawa ta shugabanni da kuma kungiyoyin zamantakewa na yankin Arewa da suka yi hangen bai cancanci jagoranci ba.
Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kawuna sun rabu tsakanin Dattijan kabilar Ibo dangane da dan takarar shugaban kasa da za su marawa baya yayin babban zabe na 2019.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng