Budurwa ta kashe saurayinta, ta dafa shinkafa jalof da namansa

Budurwa ta kashe saurayinta, ta dafa shinkafa jalof da namansa

An zargi wata mata 'yar asalin kasar Morocco da kisan masoyinta, tare da dafa namansa a cikin shinkafa jalof da ta dafa wa ma'aikata a kasar Dubai.

Matar, da ba a bayyana sunanta ba, ta aikata wannan ta'addanci ne a gidansu da ke unguwar Al Ain bayan saurayinta da su ka shafe shekaru 7 tare ya gudu wajen wata sabuwar budurwa sa 'yar kasar Dubai, a cewar dan sanda mai gabatar da kara.

Jam'ian tsaro sun ce ta datsi sassan naman jikin saurayinta tare da malkade shi a cikin wani girkin shinkafa jalof da ta yiwa wasu ma'aikata 'yan asalin kasar Pakistan da ke aiki kusa da gidanta.

'Yan sanda sun fara binciken mutuwar saurayin nata ne bayan dan uwansa ya yi korafin cewar an neme shi an rasa.

Budurwa ta kashe saurayinta, ta dafa shinkafa jalof da namansa
Budurwa ta kashe saurayinta, ta dafa shinkafa jalof da namansa
Asali: Twitter

Ko da aka tambayi matar inda saurayin nata ya ke, sai ta ce ta kore shi daga gidansu, kuma ba ta san inda ya ke ba.

Rahotanni a kasar Morocco sun bayyana cewar daga baya ne binciken ma'aikata ya kai su da gano hakorin marigayin a cikin na'urar malkada kayayyakin girki.

DUBA WANNAN: Tsaro: Rundunar soji ta gano sabuwar kungiyar ta'addanci a arewa, hotuna

Bayan an tabbatar da hakorin na marigayin ne bayan gudanar da wani gwaji na kwayoyin halitta (DNA test), sai aka kama budurwar ta sa.

A hannun jami'an tsaro ne ta amsa laifin aikata kisan mijin nata, amma ta ce hakan ta faru ne a lokacin da ba ta cikin hayyacinta. Matar ta kara da cewar ta shafe tsawon shekaru ita ke daukar nauyin bukatun mijinta na kudi tare da sanar da jami'an tsaro yadda ta biya wani abokinta wajen boye ragowar gawar tsohon saurayin nata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng