Fasa taro: Shugaban APC Oshiomole ya rikirkita mahalarta bikn kaddamar da littafin Jonathan

Fasa taro: Shugaban APC Oshiomole ya rikirkita mahalarta bikn kaddamar da littafin Jonathan

Shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole yaci gari a yayin daya fasa taro a yayin bikin kaddamar da littafin tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan daya gudana babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata 20 ga watan Nuwamba.

Legit.com ta ruwaito an jima da fara taron kaddamar da littafin kafin isar Oshiomole, amma a yayin kafarsa ta taka dakin taron sai mahalarta taron suka kwashe da sowa suna kiran “Baba oshiomole” “Baba oshiomole” ana tafi da fito.

KU KARANTA: Hukumar INEC ta bankado sunayen matattu 1,931 a rajista zaben Kaduna

Fasa taro: Shugaban APC Oshiomole ya rikirkita mahalarta bikn kaddamar da littafin Jonathan
Oshiomole da Jonathan
Asali: Twitter

Shi kuwa gogan naku binsu yayi yana daga musu hannuwa biyu biyu alamar godiya da jinjina, har ma aka jiyo sautin muryar wani daga cikin mahalarta taron yana tambaya “Wai ba Oshiomole bane wancan, me yake yi anan.?” Daga bisani Jonathan ya mike suka gaisa tare da rungumar juna, sa’annan ya zauna.

Jama’a da dama sun yi mamakin halartar Oshiomole wannan biki, duba da cewa tsohon shugaba Goodluck Jonathan dan jam’iyyar PDP ne, don haka yawancin manyan bakin da suka halarci taron abokan hamayyar Oshiomole ne, haka zalika Jonathan ya bada labarin yadda ya fadi zaben 2015 ne a littafin.

Sai dai shima tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya samu irin wannan kyakkyawar tarba daga mahalarta taron, inda shigarsa keda wuya suka fara kiran “Baba Oyoyo” “Baba Oyoyo!”

Bikin kaddamar da littafin na Jonathan yayi daidai da cikarsa shekaru sittin da daya a rayuwa, don haka aka shirya bikin a otal din Transcorp Hilton dake babban birnin tarayya Abuja, kuma ya samu halartar manya manyan mutane daga ciki daga wajen kasar nan.

Daga cikin mahalarta taron akwai tsofaffin shuwagabannin kasashen Afirka da suka hada da John Drahmani, da Koroma, sai kuma tsohon shugaban Najeriya Yakubu Gowon, tsohon alkalin alkalan Najeriya, Salisu Belgore, Sanata Bukola Saraki, Yakubu Dogara, shugaban PDP, tsofaffin gwamnoni da ministoci da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng