Yadda wata Mata ta haihu a kungurmin daji bayan barayi sun yi garkuwa da ita a Zamfara

Yadda wata Mata ta haihu a kungurmin daji bayan barayi sun yi garkuwa da ita a Zamfara

Wata Mata da yan barayin mutane suka yi garkuwa da ita ta haihu bayan kimanin awanni biyar da yan bindigan suka yi awon gaba da ita daga kauyen Danjibga dake cikin karamar hukumar Tsafe ta jahar Zamfara, inji rahoton Daily trust.

Majiyar Legit.com ta ruwaito a Juma’ar data gabata ne wasu yan bindiga suka kai farmaki a kauyen, inda suka yi awon gaba da shanu goma sha bakwai, sa’annan suka kashe wasu mutane uku da suka bi sawunsu da nufin kwato shanun.

KU KARANTA: Kurungus! Atiku ya bayyana wanda zai sayar ma kamfanin NNPC idan ya zama shugaban kasa

Wani mazaunin kauyen daya nemi a sakaya sunansa ya shaida ma majiyarmu cewa: “Yan bindiga sun kashe mutane uku sa’annan suka yi garkuwa da mutum daya da shanu goma sha bakwai, amma sun saki mutumin a ranar Asabar.

“A daren jiya ma sun sake dawowa kauyen da nufin yin garkuwa da wani dan kasuwa, amma daya fahimci shi suke nema, sai yayi caraf ya dare Katanga, inda ya haure ya cika wandonsa da iska, ya bar matansa biyu a gida.

“Da yake dama guda daga cikin matan dan kasuwan na cikin halin nakuda, amma duk da haka hakan bai hana yan bindigan yin awon gaba da ita ba, inda jim kadan bayan tafiyarsu da ita ta haifi jariri namiji.” Inji shi.

Bayan matar ta haihu ne sai barayin suka kira Alhajin suka shaida masa labarin haihuwar, inda suka bayyana masa matarsa ta samu karuwar da namiji, daga nan kuma suka kashe wayar ba’a sake samunsu a waya ba.

Da fari sai da wasu yan gungun bindiga suka kai farmaki karamar hukumar Shinkafi dake jahar Zamfara inda suka yi awon gaba da mutane Talatin a lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida bayan kammala cin kasuwar garin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel