Babban Malamin Musulunci a duniya ya ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)

Babban Malamin Musulunci a duniya ya ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin babban Malamin addinin Musulunci Sheikh Ismail Mufti Menk a wata ziyara daya kai fadar gwamnatin Najeriya, dake Aso Rock Villa babban birnin tarayya Abuja a daren Lahadi, 18 ga watan Nuwamba.

Mufti Menka da kansa ne ya bayyana ziyarar daya kai ma Buhari a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda ya jinjina ma shugaba Buhari bisa saukin kai da yake da shi, kamar yadda Legit.com ta ruwaito.

KU KARANTA: Gungun yan bindiga sun halaka hadimin gwamna da Bom a jahar Kogi

Babban Malamin Musulunci a duniya ya ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)
Menk da Buhari
Asali: Facebook

“Da yammacin yau na samu ganawa da guda daga cikin shuwagabanni mafi saukin kai da kyawun manufa, Muhammadu Buhari a Abuja.” Kamar yadda Sheikh Ismail Menk ya bayyana a shafin nasa.

A yayin ganawar da suka yi, Menk ya mika ma Buhari kyautan wasu littafai daya rubuta kuma ya wallafa da kansa, sa’annan daga karshe yayi addu’an Allah ya yi ma Buhari albarka da ma Najeriya gaba daya.

Mufti Menk ya samu rakiyan babba kuma sanannen malamin ahlussunnah, Sheikh Isa Ali Pantami, kuma kwararre a fannin ilimin kimiyyar zamani ta na’ura mai kwakwalwa, wanda a yanzu haka shine shugaban hukumar gwamnatin tarayya dake kula da cigaban cigaban kimiyya a Najeriya.

Babban Malamin Musulunci a duniya ya ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)
Pantami,Buhari da Menk
Asali: Facebook

Mufti ya ziyarci Buhari ne a karshen ziyarar daya fara kaiwa garin Maiduguri ta jahar Borno, inda ya gabatar da wa’azi a masallacin Al-Ansar da jami’ar Maiduguri don amsa gayyatar da wata kungiyar Musulunci mai suna ‘The One Ummah Group’ ta yi masa.

Haka zalika Menk ya kai ma gwamnan jahar Borno, Kashim Shettima ziyara a fadar gwamnatin jahar dake Maiduguri, inda ya jinjina ma gwamnan bisa namijin kokarin da yake yi wajen gyara jahar Borno duk da ayyukan yan ta’adda.

Shima gwamnan ya yaba ma Malamin saboda kokarin wa’azantarwa tare da wayar da kawunan al’ummar Musulmai, musamman matasa ta hanyar daura karatuttukansa a shafukan sadarwa daban daban.

Shi dai Mufti Menk yayi karatune a jami’ar Madina, amma dan asalin kasar Zimbabwe ne, inda aka haifeshi a ranar 25 ga watan Yuni na shekarar 1975, hakan ya nuna shekarunsa 43, kuma a yanzu shine babban mai bada fatawa a kasar Zimbabwe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng