APC da wasu jam’iyyu 7 sun hada karfi da karfe don yi ma PDP taron dangi a zaben jahar Kwara

APC da wasu jam’iyyu 7 sun hada karfi da karfe don yi ma PDP taron dangi a zaben jahar Kwara

Jam’iyyu guda bakwai ne suka amince su yi aiki tare da jam’iyyar APC don yi ma jam’iyyar PDP taron dangi a zaben cike gurbi na kujerar dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ekiti/Isin/Irepodun/Oke-Ero a jahar Kwara.

Majiyar Legit.com ta ruwaito hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta shirya zaben ne sakamakon mutuwar yar majalisa Funke Adedoyin, wanda take kan wannan kujera. Haka ne sanya jam’iyyun siyasa da dama suka shiga gogoriyon ganin dan takararsu ya hau wannan kujera.

KU KARANTA; Abin kunya: Wata jami’a ta haramta ma daliban jahar Kano shiga aji a kasar Sudan

APC da wasu jam’iyyu 7 sun hada karfi da karfe don yi ma PDP taron dangi a zaben jahar Kwara
Jam'aiyyar APC
Asali: Depositphotos

Sai dai a irin siyasar bukata da ake yi a Najeriya, shuwagabannin jam’iyyu guda bakwai sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar jam’iyyar APC a wannan zabe, Raheem Olawuyi, a wani taron siyasa da ya gudana a garin Omu-Aran cikin karamar hukumar Irepodun.

Jam’iyyun sun hada da: Peoples Progressives Party-PPP, National Action Council-NAC, New Progressives Movement-NPM, Peoples Redemption Party-PRP, National Democratic Liberty Party-NDLP, National Conscience Party-NCP da United Democratic Party-UDP.

Shugaban jam’iyyar PPP a jahar Kwara, Kayode Banji ya bayyana dan takarar APC Olawuyi a matsayin mutum mai amana da aminci, wanda yake da akidu irin na jam’iyyar PPP, don haka yace PPP za ta tara ma Olawuyi kuri’u, tare da fatan INEC za ta shirya zabe mai inganci.

Shima shugaban jam’iyyar NPM, Samson Olaitan ya bayyana cewa jam’iyyarsu ta yanke shawarar bin dan takarar APC a wannan zabe ne saboda ire iren ayyukan alherin da ya yi a baya, musamman a siyasan yankin.

Shi kuwa mai gayya mai aiki, Olawuyi cewa yayi a nasa jawabin yana da yakinin idan dukkanin jam’iyyun suka hada karfi da karfe, tabbas zasu samu nasara a zaben cike gurbin, sa’annan ya gode ma jam’iyyu bakwai da suka bashi goyon baya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng