Babban sufetan Yansandan Najeriya ya bayyana yawan Yansandan Najeriya

Babban sufetan Yansandan Najeriya ya bayyana yawan Yansandan Najeriya

Babban sufetan Yansandan Najeriya, IG Ibrahim Idris ya bayyana adadin Yansandan Najeriya, inda yace gaba daya Yansandan Najeriya babba da karami adadinsu shine dubu dari uku da talatin da hudu, (334,000), sune Yansandan dake aikin tabbatar da doka da oda a Najeriya.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito IG Ibrahim Idris ya bayyana haka ne a yayin dayake jawabi a taron karrama na wata kungiyar kare makarantu da aka yi a babban birnin tarayya Abuja, inda IG ya samu wakilcin kwamishinan Yansanda Olusegun Odumosu.

KU KARANTA: Abin kunya: Wata jami’a ta haramta ma daliban jahar Kano shiga aji a kasar Sudan

IG yace duk guma guman kalubalen dake addabar rundunar Yansandan Najeriya, rundunar ta samu cigaba musamman ta hanyar amfani da kayan aiki na zamani, tare da kirkiro sabbin dabarun magance matsalolin tsaro da yayi daidai da bukatar zamani.

Babban sufetan Yansandan Najeriya ya bayyana yawan Yansandan Najeriya
Yansanda
Asali: UGC

Sai dai IG ya tabbatar da cewa matsalar garkuwa da mutane na daga cikin manyan miyagun ayyuka dake ci ma yan Najeriya tuwo a kwarya, inda ake yawan samun hare haren barayin mutane a makarantun Najeriya. Amma ya danganta matsalar ga abokan hamayya a siyasa.

“Duba da bukatar tabbatar da tsaro a makarantunmu, musamman domin samar da ingantaccen yanayin koratu ga dalibai, ya dace a fara tsaron makarantun Najeriya na tsawon awanni 24, tare da samar da Yansandan da zasu dinga gudanar da sintiri a kullum a makarantar.” Inji shi.

Haka zalika IG ya yi kira da a samar da tsarin tsaro a matakin al’umma, wanda yace hakan zai rage matsalar garkuwa da mutane domin a cewarsa samar da tsaro a makarantu aiki ne daya rataya a wuyan dukkanin masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da fannin tsaro.

Bugu da kari babban sufetan ya kara da cewa sun yaba da yadda gwamnatin Buhari ke saSmar musu da isassun kudaden aiki, don haka ya tabbatar da cewa idan aka cigaba a haka zasu samu kwarin gwiwar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Daga karshe IG Ibarahim ya yaba ma mashirya taron, Safe School Academy International, wata kungiya mai zaman kanta a garin Abuja bisa namijin kokarin da take yi wajen tabbatar da tsaro a makarantu.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai wakilan hukumar NSCDC, Sojojin Najeriya, hukumar kashe gobara, masu makarantun kudi, shuwagabannin makaratun da dai sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng