Jerin sunayen jaruman Kannywood 12 da ke yiwa Atiku kamfen
- A yayin da siyasa ke cigaba da mamaya da ratsa jiki da harkokin jama'a, an yi sharhi a kan yadda goyon bayan Atiku da Buhari ya raba kan jaruman Kannywood
- Yin sharhin ya biyo bayan ganin yadda jaruman ke fitowa fili domin nuna goyon bayansu ga dan takarar da su ke ra'ayi
- Sai dai har yanzu ba a san ina fitaccen jarumi Ali Nuhu ya saka gaba ba
Sannu a hankali siyasa sai kara shiga duk sabgogi da kasuwancin jama'a ta ke yi. Irin wannan mamaya da siyasa ke yi ne ya saka jaridar Daily Trust yin wani sharhi a kan yadda goyon bayan Atiku da Buhari ya raba kan jaruman masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.
A yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, an samu rabuwar kai tsakanin jaruman masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood a kan goyon bayan manyan 'yan takarar shugaban kasa; Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da shugaba Buhari na jam'iyyar APC.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta tattaro jerin jaruman Kannywood da tuni su ka fara yiwa Atiku kamfen. Ga jerin sunayen na su:
1. Sani Danja
2. Isa Feroz Khan
3. Bashir Nayaya
4. Maryam Booth
5. Fati Muhammad
DUBA WANNAN: Yakin duniya na II: Yariman Ingila ya karrama sojojin Najeriya da suka kwanta dama, hotuna
6. Zaharaddeen Sani
7. Ummi Zee-Zee
8. Usman Mu'azu (Darekta)
9. Salisu Mu'azu (Darekta)
10. Hafizu Bello
11. Mustapha Nabruska
12. Abubakar Sani (Mawaki)
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng