Rashin biyaya ga umurnin kotu wani nau'i ne na rashawa - Sarkin Gummi

Rashin biyaya ga umurnin kotu wani nau'i ne na rashawa - Sarkin Gummi

- Sarkin Gummi, Justice Lawal Hassan ya yi korafi kan yadda gwamnatin Najeriya ke watsi da umurnin kotu da sunan yaki da rashawa

- Basaraken ya ce babu yadda za ayi demokradiya da dore mudin ana samun wasu suna saba umurnin kotu da dokokin kasa

Sarkin Gummi, Justice Lawal Hassan Gummi (murabus) ya bayyana cewa rashin biyaya ga umurnin kotu shima wani nau'i ne na rashawa inda ya bukaci gwamnati ta kasance kan gaba wajen biyaya ga umurnin kotu saboda ya zama darasi ga sauran al'umma.

Ya ce rashin biyaya ga doka, rashin shugabanci nagari, rashin biyaya ga umurnin kotu, saba ka'idojin zabe da jam'iyyu keyi da yadda iyayen gida na siyasa su kayi babakere ga harkokin siyasa yana barazana ga demokradiyar Najeriya.

Rashin biyaya ga umurnin kotu rashawa ce - Sarkin Gummi

Rashin biyaya ga umurnin kotu rashawa ce - Sarkin Gummi
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan irin tarbar da aka yiwa Buhari yayin da ya isa Paris

Sarkin ya yi fadi hakan ne a jawabin da ya yi wajen taron tsaffin daliban Kwallejin Barewa na shekara-shekara da aka gudanar a dakin taro na Umari Ali Shinkafi Polytechnic da ke Sokoto a kasidarsa mai taken "Kalubalen da bangarar shari'a ke fuskanta a cikin demokradiya a Najeriya."

Gummi ya ce bangaren shari'a itace ya kamata ta bawa demokradiyya kariya saboda idan ba haka ba, za a samu wasu bata gari da za su rika jefa al'umma cikin fargaba da fitina da yiwa demokradiya barazana.

Ya ce, "Anyi watsi da umurnin kotu duk wai da sunan yaki da rashawa. Babu wanda ya ke da ikon saba dokar kasa komin girmansa, ko da kuwa anyi hakan ne da sunan yaki da rashawa. Rashin biyaya ga umurnin kotu shima kansa rashawa ne."

"Bangaren masu mulki ba za su zama masu zargi da kuma zartas da hukunci a lokaci guda ba. Tsare kasa baya bayar da damar wani ya karya dokar kasar hasali ma dokar kasa ne ya kamata ya zama jagorar duk wani mai nufin kawo gyara."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel