Dakarun Soji sun dakile harin da 'yan Boko Haram suka kai a Katarko

Dakarun Soji sun dakile harin da 'yan Boko Haram suka kai a Katarko

Dakarun Sojin Najeriya sunyi nasarar dakile wata hari da mayakan kungiyar Boko Haram su kayi niyyar kaiwa a garin Katarko da ke Jihar Yobe.

Dakarun sojin sector 2 da ke aikin samar da zaman lafiya na Operation Lafiya Dole ne su kayi musayar wuta da 'yan Boko Haram din a garin Katarko da ke kilomita 41 arewacin garin Buni Yadi da ke jihar Yobe misalin karfe 7 na yammacin jiya 7 ga watan Nuwamba.

DUBA WANNAN: Ya kashe matar sa da yayansa bayan ya kama su turmi da tabarya

Majiyar Legit.ng Hausa ta ruwaito cewar hukumar sojin ta sake aikewa da wasu karin dakarun sojoji domin taimakawa wadanda ke garin na Katarko.

Soji sun fatattaki 'yan Boko Haram da suka kai hari a Katarko

Soji sun fatattaki 'yan Boko Haram da suka kai hari a Katarko
Source: Depositphotos

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewar wasu mayakan Boko Haram sun kai mugun samame a yankin kudancin jihar Borno a daren Talata, inda suka yi sacen sacen kayayyakin abinci, daga bisani suka banka ma duk wani gida dake kauyen wuta, suka tsere, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rahoton ya ce a sakamakon wannan harin mazauna kauyen na Kala dake kusa da karamar hukumar Damboa sun yi batan dabo, ko sama ko kasa an nemesu an rasa har bayan tafiyan yan ta’addan.

Wani shaidan gani da ido ya tabbatar ma majiyarmu cewa da misalin karfe 9 na daren Talata yan ta’addan suka kunno kai cikin kauyen, inda suka bude ma mazauna kauyen wuta irin na mai kan uwa da wabi, wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu, wasu kuma suka jikkata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel