Abubuwa 7 da ba a yarda mutum ya yi ba a kasar Saudiyya

Abubuwa 7 da ba a yarda mutum ya yi ba a kasar Saudiyya

Kasar Saudiyya ta yi suna a duniya ne saboda dalilai na addini. Miliyoyin mutane ne ke ziyartar kasar Saudiyya duk shekara domin dalilai ma su nasaba da addini.

Ragowar kasashen duniya na ganin kasar Saudiya a matsayin kasa mai dokoki ma su tsauri duk da kusanci da alaka mai karfi da ke tsakanin kasar ta Saudi da Amurka.

Sai dai a 'yan kwanakin baya bayan nan, kasar ta Saudiyya ta fara sassauta wasu daga cikin dokokinta ma su tsauri, amma har yanzu akwai abubuwan da yinsu a kasar kan iya kai mutum ga gidan yari ko haddasa ma sa matsala da jami'an tsaro.

1. Giya: Sha da siyar da giya a kasar Saudiyya doka ce. Hukuncin wanda aka kama da giya shine zaman gidan yari.

Abubuwa 7 da ba a yarda mutum ya yi ba a kasar Saudiyya
Maniyyata aikin hajji
Asali: Depositphotos

2. Cin naman alade: Naman alade da duk wani nau'in abinci ko abin sha da ke dauke da shi haramun ne a kasar Saudiya. Wanda duk aka samu da naman alade ko wani kayan kwalam da ke dauke da shi zai fuskanci fushin hukuma.

4. Fina-finan Batsa: Ba iya fina-finan batsa ba, hatta hotuna ma su nuna tsiraici ba a yarda mutum ya shiga da su kasar Saudiyya ba, ko da kuwa a wayarsa ta

5. Cudanya maza da mata: Ko a wurin sayar da kayan kwalam da makulashe layin maza daban ya ke da na mata. Namiji ba zai yi doguwar magana da mace ba a idon jama'a, musamman jami'an 'yan sanda da kan iya cajin mutum da laifin karuwanci ko niyyar aikata lalata.

6. Daukar hoton masarauta da ginin gwamnati ba tare da izini ba: Ba a yarda wani mutum ya fito da na'urar daukan hoto ya fara yin hoton fadar masarautar kasar Saudiyya ko wani gini n gwamnati ba.

DUBA WANNA: Jam'iyyar APC ta kori Inuwa Abdulkadir, mataimakin Oshiomhole

. Murnar ranar masoya (valentine's day): Yin biki ko nuna murnar domin wannan rana ta masoya laifi ne a kasar Saudiyya. Wannan doka ta samo asali ne a cikin Qur'ani, inda aka haramta yin koyi da al'adun Yahudu da Nasara.

8. Yin wani addini bayan Musulunci; Duk da akwai mabiya addinan da ba Islama ba da ke zaune a ksar Saudiyya, bayyana alamar wani addini ko mallakar wurin ibadarsa bai hlata ba a ksar Saudiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel