Jam'iyyar APC ta kori Inuwa Abdulkadir, mataimakin Oshiomhole

Jam'iyyar APC ta kori Inuwa Abdulkadir, mataimakin Oshiomhole

- Jam'iyyar APC ta kori Inuwa Abdulkadir, mataimakin Adams Oshiomhole, shugaban jam'iyyar APC na kasa

- APC ta kori Abdulkadir ne bisa zarginsa da cin dunduniyar jam'iyyar a siyasance, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito

- Da aka tuntubi Abdulkadir, ya ce ba a bi ka'ida da doka ba wajen korar da aka yi masa

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewar Abdulkadir na hannun damar Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto, ne, kuma APC ta kore shi ne bayan ya samu sabani da jagoran jam'iyyar a Sokoto, Aliyu Wammako.

A wata hira da jaridar ta yi da shugaban jam'iyyar APC a jihar Sokoto, Isa Achida, ya ce sun kori Abdulkadir saboda dalilan cin dunduniyar jam'iyya a siyasance da su ka hada da kin yin biyayya ga dokar jam'iyya, yin taro da ya saba da na jam'iyya, da kuma raini ga shugabannin jam'iyya.

Jam'iyyar APC ta kori Inuwa Abdulkadir, mataimakin Oshiomhole
Inuwa Abdulkadir
Asali: Twitter

Ya ce sun bi hanyoyin da ya dace wajen korar mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa.

DUBA WANNAN: Babban Sarki a Najeriya ya bukaci Ingila ta dawo da kayan tarihin masarautar sa

A cewar Achida, korar Abdulkadir ta samo asali ne tun daga mazabar sa, zuwa karamar hukumar sa kafin daga bisani shugabancin jiha ya amince da korar ta sa.

Da aka tuntubi Abdulkadir, ya ce ba a bi ka'ida da doka ba wajen korar da aka yi masa.

Uwar jam'iyyar APC ta kasa ba ta ce komai a kan batun ba, ya zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng