Wasu barayin mutane sun bayyana dalilin da yasa suka yi garkuwa da Uwardakinsu

Wasu barayin mutane sun bayyana dalilin da yasa suka yi garkuwa da Uwardakinsu

Wasu direbobi guda biyu sun fada komar jami’an Yansanda bayan sun yi kokarin yin garkuwa da wata Uwardakinsu, sai dai sun bayyana cewa sun yi garkuwan da itace saboda zaluncinta, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito direbobin sun hada da Emmanuel Okemiyan da Austine Anyia, kuma an daukesu aiki ne don su dinga tukar matar da mijinta, ana cikin haka ne suka gaji da halayyar da matar take nuna musu.

KU KARANTA; Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu manyan Limamai guda 4 a Delta

Sakamakon zaluntarsu da suka ce tana musu ne suka yanke shawarar yin garkuwa da ita, shirin da ya daukesu kwanaki goma suna tsara yadda zasu yi awon gaba da matar, tare da riketa har sai an biyasu makudan kudaden fansa.

Sai dai a ranar 19 ga watan Oktoba da misalin karfe 9:30 wasu suka tsegumta ma rundunar Yansandan jahar Legas cewa wasu gungun barayin mutane sun kammala shirin yin garkuwa da matar mai suna Ijeoma Eze Okafor, mashahuriyar yar kasuwa.

Da wannan bayanan sirrin da Yansandan suka samu ne ta aika jami’an rundunar SARS, wadanda suka kutsa kai cikin sansanin batrayin, inda suka yi basaja a matsayin dasu za’ayi wannan danyen aiki.

Ana cikin haka ne sai barayin suka nemi jami’an na SARS dasu samo musu motoci da bindigu, sa’annan suka mika musu hotunan matar da zasu yi garkuwa da ita, a cikin rashin sani irin nasu basu san da Yansanda suke tarayya ba.

Yansandan sun cigaba da biye ma barayin har sai ranar da suka fita da niyyar aiwatar da mummunan shirin nasu, inda Yansanda suka yi musu kawanya, suka kamasu. A jawabinda guda daga cikin direbobin ya shaida ma Yansanda, yace sun biya wani abokinsu N10,000 don neman sa’a daga wajen boka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel