Da duminsa: Zan saki bidiyon harin idan hukumar yan sanda ba tayi hattara ba – Ekweremadu ya yi barazana

Da duminsa: Zan saki bidiyon harin idan hukumar yan sanda ba tayi hattara ba – Ekweremadu ya yi barazana

Mambobin Majalisar dattijan Najeriya sun caccaki hukumar yan sandan Najeriya kan karyata ikirarin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, cewa an kai masa harine da nufin kasheshi.

A jiya, kakakin hukumar yan sanda Najeriya ya saki jawabin cewa yan fashi ne kawai suka fasa gidansa kuma basuyi nufin kashesa ba.

Sanatocin a yau Laraba sun caccaki hukumar kan jawabin da tayi ba tare da gudanar da kwakkwaran bincike ba kafin furuci.

Ekweremadu wanda ya nuna bacin ransa yace hukumar har yanzu bat binciki yan sandan dake tsareshi ba, kana basu kamo yan fashin da suka gudu ba.

Mataimakin shugaban majalisan ya yi barazanar cewa zai saki bidiyon na’urar CCTV da ya dauki yadda yan fashin suka kawo masa hari.

KU KARANTA: Yan kasuwa sun watsawa El-Rufai kasa a ido

Sanata Shehu Sani na jihar Kaduna, Dino Melaye na Kogi da Eyinaya Abaribe na jihr Abia sun tofa albarkacin bakinsu inda Shehu Sani yace akwai lauje cikin nadi.

Yan majalisar sun yanke shawarar cewa zasu gudanar da bincike mai zurfi cikin wannan al’amari.

Mun kawo muku rahoton cewa Hukumar yan sanda Najeriya ta sanar da cewa ta damke hafsoshinta hudu kan harin da aka kaiwa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, a gidansa dake Apo ranan Talata, 6 ga watan Nuwamba, 2018.

A wasikar da hukumar ta turowa Legit.ng, ta musanta cewa ta yi jinkiri wajen amsa kiran Ekweremadu yayinda aka far masa.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel