Gwamnan APC ya maka Sufeta Janar na 'yan sanda a kotu, ya nemi a biya shi N1bn
Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya yi karar sufeta janar na 'yan sanda Ibrahim Idris saboda bincike gidansa da jami'an yan sanda su kayi a jihar Plateau ba tare da izinin kotu ba.
A yayin da ya ke shigar da karar a gaban Alkali Musa Karya na babban kotun tarayya da ke Jos, gwamnan ya ce bincike a gidansa ba tare da izinin kotu ba ya keta hakkinsa na dan adam.
Gwamnan ya bukaci kotu ta tilastawa 'yan sandan biyansa N1.25 biliyan domin keta haklinsa a akayi.
A cikin karar da ya shigar, Okorocha ya yi karar kwamishinan 'yan sanda na jihar Plateau, Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC) da Attoney Janar kuma Ministan Shari'ah na kasa.
DUBA WANNAN: 'Yan kasuwa sun yiwa El-Rufai ihu, sunyi watsi da tayin da ya yi musu
Lauyan gwamnan, Markus Saleh (SAN) ya sanar da kotun cewa a ranar 3 ga watan Mayun shekarar 2018 ne aka kai samame gidan wanda ya ke karewa.
Ya yi ikirarin an tsare iyalansa da masu aiki a gidansa ba bisa kan ka'ida ba lokacin da ake bincike a gidan.
Hakan yasa Okorocha ke rokon kotun ta ayyana cewar samamen da aka kai gidansa ba bisa kan ka'ida bane saboda babu izinin yin hakan daga kotu.
Ya kuma roki kotun ta haramtawa hukumomin tsaro bincika gidajensa da ke sassan kasar nan a gaba.
Bayan sauraron karar, Alkalin kotun, Justice Kurya ya daga cigaba da shari'ar zuwa ranar 24 ga watan Janairun shekarar 2019.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng