Rundunar mayakan Sojan sama za ta kafa sansanin dakarunta a Birnin Gwari

Rundunar mayakan Sojan sama za ta kafa sansanin dakarunta a Birnin Gwari

Rundunar mayakan Sojan sama ta bayyana cewa za ta kafa sansanin Sojoji a karamar hukumar Birnin Gwaro ta jahar Kaduna domin karfafa tsaro a yankin sakamakon addabar al’umma da yan bindiga da masu garkuwa da mutane suke yi.

Majiyar Legit.com ta ruwaito babban hafsan Sojan sama, Sadique Abubakar ne ya saanr da haka a ranar Talata a yayin ziyarar da ya kai ma Sarkin Birnin Gwari, Zubairu Jibril Mai Gwari a fadarsa dake Birnin Gwari.

KU KARANTA: Yajin aiki: Malaman jami’a sun garkame wata jami’ar kimiyya da fasaha

Rundunar mayakan Sojan sama za ta kafa sansanin dakarunta a Birnin Gwari
Ziyarar
Asali: UGC

“Mun zo ne don mu tabbatar ma jama’an Birnin Gwari cewa rundunar Sojan sama zata hada kai da rundunar Sojan kasa da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da tsaro a yankin nan, zamu samar da sansani, inda jirgin sama mai tashin angulu zai iya sauka don samar da sahihin tsaro.” Inji Sadique.

Babban hafsan Sojan na sama ya cigaba da cewa: “Da zarar mun kammala bincike na karkashin kasa, mutanenmu zasu fara gina wurin da Jirgin zai dinga sauka da tashi, a shirye muke tsaf mu yaki miyagun mutane da duk wadanda ke son cutar da Najeriya.”

Iya mashal Sadique ya bayyana ma Sarkin Birnin Gwari cewa akwai wasu jirage guda 18 da gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta saya musu, yace jiragen zasu taimaka kwarai da gaske wajen samar da tsaro.

“Aiki na musamman na yaki da yan bindiga, Operation Dirar Mikiya’ da muka kaddamar da Zamfara da Katsina, zamu fadadashi zuwa Birnin Gwari.” Inji shi.

Daga karshe shima Sarki Mai Gwari ya bayyana ma godiyarsa ga rundunar Sojan sama bisa kokarin da take yi na samar da tsaro a yankin tare da tabbatar da shi, sa’annan ya bayyana farin cikinsa da kafa wannan sansani, don haka yace zasu baiwa rundunar dukkan goyon bayan da take bukata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel