Sheikh Ahmad Gumi ya nemi a rika damawa da kowane bangare a tafiyar siyasa a Najeriya

Sheikh Ahmad Gumi ya nemi a rika damawa da kowane bangare a tafiyar siyasa a Najeriya

Idan ba ku manta ba, kun samu labari cewa Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya zabi mace tayi takara a matsayin Mataimakiyar sa a APC a zaben 2019. Yanzu haka wannan mataki yana cigaba da jawo magana.

Sheikh Ahmad Gumi ya nemi a rika damawa da kowane bangare a tafiyar siyasa a Najeriya

Ahmed Gumi yayi magana game da takarar El-Rufai a 2019
Source: UGC

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi wanda Bajimin Malami ne a Jihar Kaduna yayi magana game da wannan batu inda yace ya kamata a rika tafiya da kowane mutum saboda a zauna lafiya a kasar a wannan marra da ake ciki.

Babbab Sheihin yace daga cikin manufar tsarin siyasa akwai kawo zaman lafiya ta hanyar damawa da kowane bangare a mulki. Sheikh Gumi yace ba akasariyya na yawan jama’a kuru make dubawa a siyasa ba har da kawo zaman lafiya.

KU KATANTA: Ba mu yi wa Abokiyar takarar El-Rufai mubaya’a ba – Kudancin Kaduna

Malamin ya bayyana cewa dole masu mulki su rika la’akari da sauran mutane daban-daban da ake da su a cikin al’umma tare da kokarin janyo su a jika domin kowa ya ji cewa ana damawa da shi a matsayin sa na Asalin mutumin kasa.

A wannan dalili na a zauna lafiya ne fitaccen Malamin yake ganin ya kamata ‘Yan siyasa su rika raba tikiti tsakanin Musulmai da Kirista a irin su Jihohin Filato Benuwai, Taraba, da kuma Jihar Kaduna inda ake da Musulmai da Kiristoci.

A halin yanzu dai Kiristoci ne kurum ke yin mulki a Jihar Benuwai da Taraba, haka-zalika a Jihar Filato, Musulmai ba su rike mukamin Mataimakin Gwamna duk da cewa su na da yawa kwarai a Jihar ta Arewa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel