Yaki da ta'addanci: Masari ya ja kunnen sarakunan jihar Katsina

Yaki da ta'addanci: Masari ya ja kunnen sarakunan jihar Katsina

- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya gargadi ma su rike da sarautun gargajiya da su guji bayar da mafaka ga 'yan ta'adda

- Masari ya yi wannan gargadi ne ta cikin wani sako mai dauke da sa hannun Abdu Lawan, mai taimaka masa a bangaren yada labarai

- Kazalika ya gargadi wadanda ke da alhakin bawa jama'a tsaro da su tabbatar sun yi aikinsu bisa gaskiya da rikon amana

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya gargadi ma su rike da sarautun gargajiya da su guji bayar da mafaka ga 'yan ta'addar da dakarun soji ke fatattaka daga jejin jihar.

Masari ya yi wannan gargadi ne a yau ta cikin wani sako mai dauke da sa hannun Abdu Lawan, mai taimaka masa a bangaren yada labarai.

Ya bayyana cewar Masari ya furta hakan ne yayin ganawar sa da ma su ruwa da tsaki a ziyarar da ya kai kananan hukumomin Danmusa, Safana, da Batsari.

Yaki da ta'addanci: Masari ya ja kunnen sarakunan jihar Katsina
Aminu Masari
Asali: Depositphotos

Kazalika ya gargadi wadanda ke da alhakin bawa jama'a tsaro da su tabbatar sun yi aikinsu bisa gaskiya da rikon amana.

"Gwamnati ba zata yarda da sakaci da aiki ba a kowanne bangare. Duk wanda ya san aikinsa ne kare al'umma, dole ya yi hakan bisa jazircewa da sadaukarwa," a cewar gwamna Masari.

Ko ranar 1 ga watan Nuwamba sai da jaridar Legit.ng ta kawo ma ku labarin cewar fiye da mutane 1,000, maza da mata, su ka tashi daga kauyen Damburawa tare da komawa fadar hakimin Batsari a jihar Katsina bayan samun barazana daga 'yan bindiga.

DUBA WANNAN: Likita ya fadi matacce bayan yiwa mutane hudu tiyata a jere

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya bayyana cewar 'yan bindigar sun kai hari kauyen amma sai jama'ar garin su ka dakile harin tare da kama biyu daga cikin maharan.

Alhaji Mansur Muaza, shugaban rikon kwarya na karamar Batsari, ya shaidawa manema labarai a yau, Alhamis, cewar 'yan bindigar sun aiko da takardar barazanar cewar za su dawo daukan fansa.

Muaza ya bayyana cewar karamar hukumar ce ke ciyar da mutanen tun bayan yin hijirar su daga kauyen ranar Laraba.

samar da wasu jami'an tsaro da ke gadin jama'ar kauyen da yanzu haka ke zaman gudun hijira a fadar hakimi," in ji Muaza.

Shugaban karamar hukumar ya bukaci 'yan gudun hijirar su kwantar da hankalinsu tare da tabbatar ma su da cewar gwamnatin jihar Katsina za ta tabbatar da tsaron lafiyar su da dukiyoyin su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng