Peter Obi ya kai wa Sanata Rabiu Kwankwaso ziyara a Abuja

Peter Obi ya kai wa Sanata Rabiu Kwankwaso ziyara a Abuja

Mun samu labari cewa Mista Peter Obi wanda shi ne ‘Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa na babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a 2019 ya gana da Sanatan Kano ta tsakiya Rabiu Musa Kwankwaso a gidan sa.

Peter Obi ya kai wa Sanata Rabiu Kwankwaso ziyara a Abuja
Peter Obi yayi wani zama da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Twitter

Peter Obi wanda shi ne Abokin Takarar Atiku Abubakar a zabe mai zuwa na 2019 ya kai wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ziyara ne har gidan sa da ke Unguwar Maitama a cikin babban Birnin Tarayya Abuja a Ranar 4 ga Watan yau.

Wani Hadimin Sanatan na Kano ta tsakiya Saifullahi Hassan shi ne ya bayyana mana wannan a shafin sa na sadarwa na zamani. Sai dai har yanzu ba mu san abin da aka tattauna tsakanin ‘Dan takarar da kuma fitaccen Sanatan ba.

KU KARANTA: An fadawa Buhari cewa akwai bukatar a binciki Gwamnan Kano

Tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso yana cikin wadanda su ka nemi takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP amma ya sha kashi a wajen zaben fitar da gwani da aka yi a hannun tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar.

Kafin wannan ganawa da aka yi a karshen makon nan, tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso da dinbin mutanen sa sun gana da Atiku Abubakar har gida da kuma Peter Obi bayan Jam’iyyar PDP ta ba Atiku tikitin takara a zaben na 2019.

Ibrahim Shekarau wanda ya taba yin Gwamna a Jihar Kano ya bayyana cewa kuri’un Shugaba Buhari za su ragu a Arewa sannan kuma yace Sanata Rabiu Kwankwaso zai yi da-na-sani bayan zaben 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel