Kuma dai: APC ta kara watsa ma shuwagaban gwamnonin APC kasa a ido
Da alama rikicin jam’iyyar APC bai kama hanyar zuwa karshe ba, musamman ta yadda uwar jam’iyyar ta kwace takarar gwamnan jahar Imo daga hannun surukin gwamnan jahar Imo, Rochas Okorocha, Ugwumba Uche Nwosu, inji rahoton jaridar Daily Trust.
Majiyar Legit.com ta ruwaito a ranar Juma’a 2 ga watan Nuwamba ne uwar jam’iyyar ta mika sunan Sanata Hope Uzodinma ga INEC, wanda shine dan takarar da kwamitin shirya zaben fidda gwani na jahar a karkashin jagorancin Ahmed Gulak ta sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
KU KARANTA: Tinubu ya kai ma Hameed Ali ziyarar jaje bayan mutuwar Uwargidarsa
Hakazalika sahihan majiyoyi sun tabbatar da cewa duk da rikita rikitan da ya biyo bayan zaben da aka yi a ranar 1 ga watan Oktoba, amma uwar jam’iyyar ta amshi sakamakon bayan dogon nazari da mahukuntan jam’iyyar suka yi.
Sai dai bayan zaben na ranar 1 ga watan Oktoba, jam’iyyar ta sake shirya wani zaben a ranar 6 ga watan Oktoba, indaasamun rahoton kwamitin sauraren korafi a karkashin jagorancin Ibrahim Agbabiaka, wanda ya bayyana Uche Nwosu a matsayin halastaccen dan takara.
Amma fa majiyar ta bayyana cewa a lokacin da wakilinta ya garzaya ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, don jin ta bakin hukumar, sai wani jami’inta ya mayar musu da martani akan cewa har yanzu basu fitar da sunayen ba.
A wani hannun kuma, wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta yi kira ga uwar jam’iyyar APC da ta bata zazzage gamsassun bayanai dake zata hanata hukunta jam’iyyar bisa yin watsi da umarnin da ta bayar na APC ta mika sunan Nwosu ga INEC a matsayin dan takarar gwamnan jahar Imo a zaben 2019.
Idan za’a tuna, Gwamna Rochas yayi alkawarin ba zai fita daga APC ba duk runtsi duk wuya duk da abinda aka yi masa, saboda a cewarsa shine ya kafa APC, don haka ba zai fita daga gidan daya gina ba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng