INEC: Mun shirya jerin sunayen ‘Yan takarar mu – Inji APC

INEC: Mun shirya jerin sunayen ‘Yan takarar mu – Inji APC

Mun samu labari cewa Jam’iyyar APC da ke mulki a Najeriya ta shirya sunayen wadanda za su yi mata takara a babban zaben da za ayi a 2019. Yanzu dai Jam’iyyar ta shirya mikawa Hukuma jerin ‘Yan takaran ta.

INEC: Mun shirya jerin sunayen ‘Yan takarar mu – Inji APC
Jam'iyyar APC ta kammala shirin jerin 'Yan takaran 2019
Asali: Depositphotos

A jiya ne Jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa ta gama shirya sunayen wadanda za su rike mata tuta a zabukan da za ayi na Gwamnoni da ‘Yan Majalisun Tarayya da na Jihohi kamar yadda dokar kasa da tsarin zabe ya tanada.

Yanzu dai an mikawa Majalisar aikace-aikace watau NWC ta Jam’iyyar APC jerin ‘Yan takaran 2019. Kafin nan Jam’iyyun kasar sun mika sunayen wadanda za su yi masu takara a 2019 a gaban Hukumar zabe na kasa na INEC.

KU KARANTA: Wani babban Sakataren PDP a Arewa ya fice daga Jam'iyyar

Hukumar zabe na INEC ta bada damar sake sunayen ‘Yan takara kafin a shiga filin zabe. INEC ta bada har zuwa Ranar 17 ga wannan Watan a matsayin lokacin da za a iya sauya sunayen ‘Yan takaran Majalisa da Shugaban kasa.

Haka kuma za a iya sauya sunan wadanda za su yi takarar Majalisar dokoki da kuma kujerar Gwamna har a Ranar farko na Watan Disamba. Har yanzu APC dai ba tace komai game da Jihar Zamfara inda INEC ta hana APC takara ba.

Daily Trust ta rahoto cewa an hangi irin su Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai da Takwaran sa na Jihar Adamawa Jibrilla Bindow a ofishin Jam’iyyar APC inda su ke kokarin ganin an aika sunayen ‘Yan takarar su gaban INEC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng