Sam Adams Oshiomhole bai yi mana adalci a Jam’iyyar APC ba – Amosun

Sam Adams Oshiomhole bai yi mana adalci a Jam’iyyar APC ba – Amosun

Yayin da ake cigaba da kokarin dinke barakar da ke cikin Jam’iyyar APC, Bola Tinubu wanda jigo ne a Jam’iyyar mai mulki sun gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari jiya tare da Shugaban APC.

Sam Adams Oshiomhole bai yi mana adalci a Jam’iyyar APC ba – Amosun
APC ta tsaida Abiodun a Ogun yayin da Gwamna ke tare da Akinlade
Asali: Facebook

Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha yayi karin haske game da abin da ke faruwa a APC jiya bayan ya gana da Shugaban kasa a sakamakon zaman da aka yi da su Tinubu inda yace babban Jigon Jam’iyyar bai san abin da yake faruwa ba.

Ibikunle Amosun ya nuna cewa babu shakka Adams Oshiomhole bai yi adalci a Jam’iyyar APC ba. Gwamnan na Jihar Ogun ya nuna cewa yana tare da Takwaran sa na Jihar Imo wajen yin tir da zabukan da APC ta gudanar a wasu Jihohin.

KU KARANTA: Saraki tsoma baki kan rikicin da ya barke a APC da su Amosun

Gwamnan yace akwai tsantsagwaron rashin adalci da bin gaskiya a zabukan fitar da gwani da aka yi kwanakin baya. Amosun ya ba Shugaban Jam’iyyar APC laifi wajen wannan danyen aiki da yake zargi an yi a Jam’iyyar mai mulkin kasar.

Bola Tinubu ya goyi bayan abin da Shugaban APC na Kasa Adams Oshiomhole yake yi inda yace Shugaban Jam’iyyar yayi bakin kokarin sa kuma babu maganar a tsige sa daga kujeran sa kamar yadda wasu Gwamnonin na Jam’iyyar APC ke kira.

Amosun yayi kaca-kaca da Oshiomhole wanda yace yaudarar yake Jama’a game da abin da ya wakana a wasu Jihohin na APC. Rikicin dai ya fi kamari ne a irin su Ogun inda aka tsiada wanda Gwmana bay ya so da kuma irin su Jihohin Imo, da Zamfara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel