Dole shugaba Buhari ya daina kisa da takurawa 'yan shia - Dr. Leo Igwe, shugaban Mulhidan Najeriya

Dole shugaba Buhari ya daina kisa da takurawa 'yan shia - Dr. Leo Igwe, shugaban Mulhidan Najeriya

- Ya zama wajibi Buhari ya dakatar da zubar da jinin yan Shi'a da akeyi

- Gwamnatin sa ta dauki yan Shi'a tamkar wasu masu laifi

- An kulle shugaban su tsayin wasu shekaru

Dole shugaba Buhari ya daina kisa da takurawa 'yan shia - Leo Igwe
Dole shugaba Buhari ya daina kisa da takurawa 'yan shia - Leo Igwe
Asali: Twitter

Wannan yanki ne na jawabi da ja-gaban marasa addini na Najeriya, watau Nigeria Humanists Association ya gabatar, kan jawo hankalin gwamnati ta daina kashe 'yan shia:

"Ya kamata shugaban kasa Muhammad Buhari ya kawo karshen zubda jinin yan Shi'a da akeyi a fadin kasar nan."

Dole shugaba Buhari ya daina kisa da takurawa 'yan shia - Dr. Leo Igwe, shugaban Mulhidan Najeriya
Dole shugaba Buhari ya daina kisa da takurawa 'yan shia - Dr. Leo Igwe, shugaban Mulhidan Najeriya
Asali: Facebook

"Tunda ya hau mulki a shekara ta 2015 bai boye tsanar da yakewa 'yan Shi'a ba, gwamnatin sa tana daukar su tamkar wasu masu laifi wadanda basu da 'yanci.

An dakatar dasu daga yin tattaki daga Kaduna zuwa Abuja don neman 'yancinsu, jami'an tsaro suna kashe su a fadin kasar nan.

Sannan an kama shugaban su Ibrahim Elzakzakiy tsawon wasu shekaru an hana a sakeshi." Dr. Leo Igwe ya Fadi, bayan da yadda ake zub da jinin jama'ar su.

DUBA WANNAN: Suna son kashe ta don ta zagi annabi

"Duk wani dan Shi'a da aka kama da laifi a gurfanar dashi a gaban kotu bawai a harbeshi akan titi ba, ya kamata a girmama bukatun su.

Shi'a yan Najeriya ne ya zama dole a mutuntasu kuma a basu girman su" ya sake bayyanawa.

Masu bin tsarin Humanism din dai, suna son a baiwa kowa 'yancin yin addininsu ko barinsa, muddin bai saba da dokar zamantakewa ba.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng