Ni ne na kafa APC, ba kuma zan fita daga cikinta ba - Gwamnan jam'iyyar

Ni ne na kafa APC, ba kuma zan fita daga cikinta ba - Gwamnan jam'iyyar

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya karyata jita-jitar da wasu ke yadawa na cewa zai fice daga jam'iyyar APC sakamakon rikicin zaben cikin gida na gwamna da ke faruwa a jihar.

A hirar da ya yi da manema labarai a gidan gwamnati bayan ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari a yau Alhamis, Okorocha ya bayyana cewa ziyarci shugaban kasa ne domin tattauna wasu abubuwa da Adams Oshiomhole ke yi a wasu jihohi.

"Ba zai yiwa in gina gida ba sannan daga baya in bar ma wasu su kwace gidan, Ina nan daram a APC, ni ne na kirkiri sunan APC saboda haka jam'iyyar mu ne kuma zamu cigaba da aiki domin cigaban jam'iyyar," inji Okorocha.

Ni ne na kafa, ba kuma zan fita daga cikinta ba - Gwamnan jam'iyyar
Ni ne na kafa, ba kuma zan fita daga cikinta ba - Gwamnan jam'iyyar
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Wasu 'yan bindiga sun sace wani babban soja

Okorocha ya ce abubuwan da Oshiomhole ke aikatawa na raba kawunnan 'ya'yan jam'iyyar inda ya kara da cewa babu hannun shugaba Buhari cikin tabargarzar da Oshiomhole ke aikatawa.

"Oshiomhole yana gaban kansa ne kawai, fadar shugaban kasa ba ta bashi goyon baya cewar ya kwace tikitin zabe daga hannun wadanda su kayi nasara ya mika wa wadanda suka fadi zabe ba.

"Ina kira da Oshiomhole ya rika biyaya ga doka da kuma biyaya da umurnin kotu a wuraren da suka dace, ba dai-dai bane jam'iyya ta rika watsi da umurnin kotu.

"Ya zama dole mu dauki mataki domin kiyaye mutunci da kimar jam'iyyar mu saboda zuwarsa ya kamata ya kawo farin ciki ne amma akasin hakan ke faruwa yanzu," inji Okorocha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164