Taran aradu da ka: Gungun masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wani Soja
Rundunar Yansandan jahar Delta ta sanar da sace wani jami’in Soja da wasu yan bindiga suka yi akan hanyar Bini zuwa Sapele ta jahar Delta, da nufin yin garkuwa da shi domin amsan kudaden fansa, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.
Majiyar Legit.com ta bayyana cewa yan bindigan sun sace Sojan ne mai suna Kola, yayin dayake kan hanyarsa ta zuwa Bini bayan ya kammala wani kwas da aka shirya ma Sojojin ruwa a garin Sapele.
KU KARANTA: Kwan gaba kwan baya: Najeriya ta rikito daga jerin kasashen da suka fi saukin hada hadar kasuwanci
Bayan sun kama shi ne sai suka wuce da shi zuwa cikin wani kungurmin daji, inda a yanzu haka sun fara tuntubar iyalansa akan sai sun biya kudi naira miliyan hudu kafin su sake shi, idan ba haka ba kuma zasu halaka shi.
Mukaddashin kaakakin rundunar Yansandan jahar, DSP Andrew Aniamaka ya bayyana ma majiyarmu cewa a rundunar na iya bakin kokarinta na ganin ta ceto rayuwar kola, inda yace tuni jami’an Yansanda suka mamaye dajin.
“Mun samu rahoton satar wani mutumi Sojan ruwa mai suna Ominiyo K.D, ganin karshe da aka masa shine a ranar 29 ga watan Oktoba da yamma a lokacin da yake cikin motarsa kirar Toyota Picnic daga kwalejin injiyan Sojan ruwa.
“A yanzu haka yan bindigan sun kira iyalansa da tsohon lambar wayarsa suna neman a basu kudin fansa naira miliyan hudu, Yansanda na aiki tukuru tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro domin ceto shi, tare da kama barayin.” Inji DSP Andrew.
Idan za’a tuna wasu gungun barayin mutane sun taba sace wani babban jami’in Sojan kasa a garin Kaduna, a lokacin da yake tare da matarsa suna hanyar zuwa unguwa, inda daga bisani sai dai gawarsa aka tsinta ta fara rubewa. Allah Ya shiga tsakanin nagari da mugu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng