Rahama Sadau ta iya motsa jiki, duba hotuna

Rahama Sadau ta iya motsa jiki, duba hotuna

Wasu hotunan jarumar masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood, Rahama Sadau, na motsa jiki da jaridar Legit.ng ta ci karo da su a dandalin sada zumunta ta yanar gizo, sun sa haifar da cece-kuce da cacar baki a tsakanin maza.

A yayin da wasu mazan ke nuna jin dadinsu daganin yadda jarumar ke motsa jiki domin kulawa da lafiyar jikinta, wasu sun bayyana mabanbancin ra'ayi.

Hotunan jaruma Rahama Sadau na motsa jiki sun gigita maza
jaruma Rahama Sadau na motsa jiki
Asali: Twitter

Hotunan jaruma Rahama Sadau na motsa jiki sun gigita maza
Jaruma Rahama Sadau
Asali: Twitter

Hotunan jaruma Rahama Sadau na motsa jiki sun gigita maza
Jaruma Rahama Sadau
Asali: Twitter

Samun maza, musamman matasa, na yin tsokaci a kan fitattun mutane, musamman jaruman fim da mawaka, ba bakon abu ba ne.

Wasu daga cikin masu bayyana ra'ayinsu a kan hotunan sun nuna matukar soyayyar su gare ta, har ta ki ga wasu na rokon ta daure ta aure su.

Wani daga cikin irin maza cewa ya yi, "da kyau Rahama Sadau, motsa jiki abu ne mai kyau, kuma matukar mace na son dadewa ba ta tsofe ba, dole ta rungumi motsa jiki. kin yi daidai.

DUBA WANNAN: Wasiyyar Gaddafi ga 'ya'ynsa mata kafin a kashe shi

Babu wani cikakken bayani a kan yaushe ne jarumar ta dauki hotunan ko kuma wurin da aka dauke su ba, illa dai an ga jarumar sanye da makaran kunne da ke kai sauti tana motsa jikinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng