Manyan ayyukan more rayuwa 5 da Buhari yayi ma jama’an Legas
Kamar yadda ake tsammani daga wajen kowanne shugaban na game da gudanar da ayyukan cigaba ga jama’ansa, haka ne tsammanin da yan Najeriya ke da shi akan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya dare madafan iko a ranar 29 ga watan Mayu.
Daga cikin jihohin Najeriya masu muhimmanci akwai jahar Legas, jahar da tafi kowace jaha arziki a Najeriya, kuma jaha ta biyu wajen yawan jama’a a Najeriya, bayan jahar Kano, kaar yadda alkalummar hukumar kidaya suka nuna.
KU KARANTA Hadarin jirgin sama a kasar Ingila ta halaka wani mai mallakin kungiyar kwallon kafa ta Leicester
Haka zalika jahar Legas na da muhimmanci a siyasance, kusan ita ce daya tilo da ta kwashe shekaru 16 tana karkashin jam’iyyar adawa, ma’ana jam’iyyar PDP bata taba mulkar jahar ba, kuma da tsohon gwamnan jahar, Tinubu aka kafa jam’iyyar APC.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu kuri’u dubu bakwai da casa’in da biyu da dari hudu da sittin a yayin zaben shekarar 2015, wanda shine sakamako mafi kyauwu da Buhari ya taba samu a jahar tunda ya fara tsayawa takara.
Wasu daga cikin manyan ayyukan da gwamnatin shugaba Buhari ta yi a jahar sun hada da;
Mika tsohon fadar gwamnatin kasa ga gwamnatin jahar Legas
Aikin gina hanyar rukuni na daya da na biyu na babban titin Legas zuwa Ibadan
Aikin gina layin dogo mai tsawon kilomita 151 daga Legas zuwa Ibadan
Aikin sanya wuta a kafatin shagunan dake kasuwar Sura
Daukan dubun dubatan matasa aiki a karkashin N-Power
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng