Hadarin jirgin sama a kasar Ingila ta halaka wani mai mallakin kungiyar kwallon kafa ta Leicester

Hadarin jirgin sama a kasar Ingila ta halaka wani mai mallakin kungiyar kwallon kafa ta Leicester

Mai mallakin kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila dake fafatawa a gasar Premier League, Vichai Srivaddhanaprabha ya rasu a ranar Asabar, 27 ga watan Oktoba a hadarin jirgin sama mai tashin angulu, jim kadan bayan ya kammala kallon kwallo.

Wannan hadari ya rutsa da Vichai Srivaddhanaprabha ne da wasu ma’aikatansa guda biyu, fasinja daya da kuma matukin jirgib, inda jirgin ya kwace ma matukinsa, mintuna kadan bayan sun tsallake filin kwallon Leicester, King Power Stadium.

KU KARANTA: Batun takardun karatun Buhari ya bar baya da kura: Amma mai kundin tsarin mulki yace?

Hadarin jirgin sama a kasar Ingila ta halaka wani mai mallakin kungiyar kwallon kafa ta Leicester
Vicha
Asali: Facebook

Majiyar Legit.com ta rundunar Yansandan garin sun bayyana cewa wadanda suka mutu a hadarin sun hada ne da ma’aikatan Vichai, Nurara Suknamai, Kavepon Punpare, matukin jirgin kuma sunansa Eric Waffer da abokiyar Vichai izabela Roza Lechowicz.

Sai dai rahotanni sun bayyana Eric Waffer a matsayin kwararren matukin jirgi, wanda ya kwashe sama da shekaru 20 yana tuka jirgin sama da mai saukan agulu, haka zalika yana tuka jirgin sama don daukar rahotanni a gidan talabijin na Channel 14.

Hadarin jirgin sama a kasar Ingila ta halaka wani mai mallakin kungiyar kwallon kafa ta Leicester
mamatan
Asali: Facebook

Shi kuwa Mista Vichai, biloniya ne na fitar hankali mai shakaru 60 a rayuwa, yana da mata da yara hudu, kuma a shekarar 2010 ya sayi kungiyar kwallon kafa ta Leicester City akan kudi pam miliyan 39, inda a shekarar da ya fito dasu daga rukunin yan dagaji zuwa rukunin zakaru suka lashe kofin Premier.

A wani labarin kuma, wani babban jirgin sama JT-610, ya gamu da hatsari a kasar Indonesia jim kadan bayan tashin yayin da yake cike makil da fasinjoji 189, a lokacin daya nufi Pangkal Pinang, wani tsibiri dake Arewacin Indonesia.

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa kowa da kowa dake cikin jirgin nan ya rasu, bayan jirgin ya samu matsala, inda ya kwace ma matukinsa, ta tunjuma cikin tekun Java, bayan akalla mintun 13 da tashinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel