2019: Saraki, Atiku, Secondus, Obi sun tafi dauro damara a Dubai

2019: Saraki, Atiku, Secondus, Obi sun tafi dauro damara a Dubai

A yayin ci gaba da yunkuri na daura damara da zage dantsen jam'iyyar PDP ta fatattakar shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kujerarsa a zaben 2019, wasu jiga-jigai na jam'iyyar sun shilla Dubai domin cimma wannan kudiri.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, kusoshin jam'iyyar za su gudanar da wata muhimmiyar ganawa a tsakanin su domin kawata shirin su da tsare-tsare yayin da yakin neman zabe zai kankama a cikin fadin kasar nan a ranar 14 ga watan Nuwamba.

Manufar wannan yunkuri na jam'iyyar da ta fara aiwatarwa a ranar Alhamis din da ta gabata can daular Larabawa bai wuci shimfida tsare-tsare na galaba kan shugaba Buhahi yayin babban zabe na badi.

2019: Saraki, Atiku, Secondus, Obi sun tafi dauro damara a Dubai
2019: Saraki, Atiku, Secondus, Obi sun tafi dauro damara a Dubai
Source: Depositphotos

Kusoshin jam'iyyar da suka shilla Dubai domin kaddamar da shirye-shiryensu sun hadar da; dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar, shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki, shugaban jam'iyyar na kasa Prince Uche Secondus da kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi.

Kazalika shugaban kungiyar yakin neman zabe ta Atiku, Gbenga Daniel, wanda shine tsohon gwamnan jihar Ogun ya halarci taron kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Gwamna El-Rufa'i ya ziyarci wasu yankuna cikin Birnin Jihar Kaduna domin tabbatar da an kiyaye dokar hana zirga-zirga

Rahotanni sun bayyana cewa, akwai yiwuwar nan da 'yan makonni kadan ma su gabatowa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar zai gabatar da tsare-tsarensa da manufofin shugabanci ga al'ummar kasar nan.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, 'yan bindiga sun sace wasu Malamai biyar na Addinin Kirista a karamar hukumar Issele-Uku ta jihar Delta a yankin Kudancin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.legit.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng