Muhimman ayyuka 4 da gwamnatin Buhari ta yi ma al’ummar jahar Kano
Masu iya magana na cewa don samun lada ake yin Sallah, kuma dama ai ladar siyasa a duniya ake samunta, musamman idan jama’a suka jajirce suka baiwa dan takarar da suke kauna dimbin kuri’un da suka kai shi ga nasara, ya zama wajibi ya biya su da alheri.
Da wannan ne LEGIT.com ta bibiye yiwuwar samu ko rashin wata tagomashi da kanawan dabo suka samu daga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, musamman duba da cewa Buharin bashi da wata jahar dake nuna masa tsananin kauna kamar Kano a duk Najeriya!
KU KARANTA: Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar PDP ya bayyana dalilin ficewa daga jam’iyyar

Asali: Facebook
Baya ga alakar Buhari da kanawa a siayasance, jahar nada matukar muhimmanci ga siyasar Najeriya, sakamakon tarin al’umma da Allah ya azurtata da shi, don haka duk wani dan siyasa dake muradin zaa shugaban kasa dole ya nemi kanawa.
Sai dai dayake soyayyar Buhari da kanawa ba karama bace, hakan ne yasa shi samun kuri’I miliyan daya da dubu dari tara da uku, da dari tara da casa’in da tara (1,903,999), da wannan ne Buhari yayi ma shugaba mai ci na wancan zamani Goolduck Jonathan fintinkau a sakamakon zaben gaba daya.

Asali: Facebook
Don haka hankali ma kadai ya isa ya sa kowa yayi tunanin Buhari ba zai manta da kanawa ba, musamman wajen kawo musu ababen cigaba da mare rayuwa, anan ma an yi sa’a shima Buharin dan halas ne, don haka ga wasu daga cikin manyan ayyuka
- Aikin sanya wuta a shagunan dari biyar (500) a kasuwar sabon gari
- Gina manyan gidaje masu sauki don amfanin ma’aikata
- Cigaba da aikin fadada hanyar Kano zuwa Maiduguri
- Daukan matasa dubu goma sha bakwai (17,000) aikin N-Power
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng