Hotunan 'yan kabilar Berom da su ka kashe janar Idris Alkali

Hotunan 'yan kabilar Berom da su ka kashe janar Idris Alkali

A yau ne hukumar 'yan sanda a jihar Filato ta fitar da jerin sunayen wasu mutane 8 da ta ke nema ruwa a jallo bisa zarginsu da kashe manjo janar Idris Alkali.

Tun a ranar 3 ga watan Satumba ne aka bayyana cewar marigayi janar Alkali ya bata bayan ya bi ta cikin garin Jos a hanyar sa ta zuwa Bauchi daga Abuja.

Bayan bincike mai zurfi da hukumar soji ta gudanar, ta gano motar janar Alkali a karkashin wani kududdufi mai zurfin gaske a yankin Dura Du da ke karkashin karamar hukumar Jos ta kudu.

Daga cikin mutanen da hukumar 'yan sanda ta bakin DSP Tyopev Tarneer, kakakinta a jihar Filato, ta bayyana na da alaka ta kai tsaye da kisan janar Alkali su ne;

1. Da Chuwang Samuel, da aka fi sani da Morinho, mai shekaru 28 na haihuwa. Hukumar 'yan sanda ta ce yana iya yin yaren Hausa da na Berom kuma yana sana'ar gyaran mota ne. 08063644429 ita ce lambar wayar sa.

Hotunan 'yan kabilar Berom da su ka kashe janar Idris Alkali

Da Chuwang Samuel
Source: Twitter

2. Nyam Samuel, da aka sani da 'Soft Touch, mai shekaru 25. Ya iya yaren Hausa, Berom da kuma Turanci.

Hotunan 'yan kabilar Berom da su ka kashe janar Idris Alkali

Nyan Samuel
Source: Twitter

3. Mathew Wrang, wanda aka fi sani da Amesco, mai shekaru 27. Ya iya yaren Hausa, Berom da Turanci.

Hotunan 'yan kabilar Berom da su ka kashe janar Idris Alkali

Mathew Wrang
Source: Twitter

4. Pam Gyang Dung, wanda aka fi sani da Boss, mai shekaru 53 a duniya. Yana da sanko kuma ya iya yaren Berom, Hausa da Turanci.

Hotunan 'yan kabilar Berom da su ka kashe janar Idris Alkali

Pan Huang Dung
Source: Twitter

5. Chuwang Istifanus Pwajok Stephen, wanda aka fi sani da Tifa, mai shekaru 46 a duniya. Dan asalin kabilar Berom ne amma ya iya Hausa da Turanci sosai.

Hotunan 'yan kabilar Berom da su ka kashe janar Idris Alkali

Chuwang Istifanus
Source: Twitter

6. Timothy Chuan, direban mota (tifa) dan asalin kabilar Berom. Ya iya yaren Hausa da Turanci sosai. 09081177173, ita ce lambar wayar sa.

Hotunan 'yan kabilar Berom da su ka kashe janar Idris Alkali

Timothy Chuan
Source: Twitter

7. Moses Gyang, wanda aka fi sani da 'Boss', mai shekaru 25. Yana tara suma a kansa, sannan yana da tsawo. Dan asalin kabilar Berom ne amma ya iya Hausa da Turanci sosai.

Hotunan 'yan kabilar Berom da su ka kashe janar Idris Alkali

Moses Gyang
Source: Twitter

8. Yakubu Rap, hakimin yankin Dura, mai shekaru 52. Dan asalin kabilar Berom ne amma ya iya Hausa da Turanci sosai.

Hotunan 'yan kabilar Berom da su ka kashe janar Idris Alkali

Hotunan 'yan kabilar Berom da su ka kashe janar Idris Alkali
Source: Twitter

Hukumar 'yan sanda ta bukaci duk wanda ya ga daya daga cikinsu da ya kira daya daga cikin lambobin da ke sama, a jikin hoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel