Bidiyon Ganduje: Jafar Jafar ya isa majalisar dokokin jihar Kano, hoto

Bidiyon Ganduje: Jafar Jafar ya isa majalisar dokokin jihar Kano, hoto

Jafar Jafar, mai kamfanin jaridar Daily Nigerian da ta fara sakin faifan bidiyon gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, na karbar daloli ya bayyana a majalisar dokokin Kano a yau, Alhamis.

An saka ran Jafar zai gana da kwamitin da majalisar ta kafa a ranar 15 ga watan Oktoba domin binciken faifan bidiyon da ke nuna gwamna Ganduje na karbar wasu makudan daloli da ake zargin cin hanci ne daga hannun 'yan kwangila. Jaridar Daily Nigerian ta Jafar Jafar ce ta fara wallafa faifan bidiyon.

Bidiyon Ganduje: Jafar Jafar ya isa majalisar dokokin jihar Kano, hoto
Jafar Jafar ya isa majalisar dokokin jihar Kano
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Adadin kudin yakin neman zabe da dokar Najeriya ta amincewa 'yan takara kashewa

Gabanin isowar Jafar, an tsaurara matakan tsaro a harabar majalisar da ma filin tashi da saukar jiragen sama na Kano domin tabbatar da tsaron lafiyar sa.

Bidiyon Ganduje: Jafar Jafar ya isa majalisar dokokin jihar Kano, hoto
Jafar Jafar ya isa majalisar dokokin jihar Kano
Asali: Twitter

Bidiyon Ganduje: Jafar Jafar ya isa majalisar dokokin jihar Kano, hoto
Jafar Jafar ya isa majalisar dokokin jihar Kano
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng