Jama'ar gari sun kori sarkinsu sukutum saboda babban laifi da suka ce ya aikata
- Wani hari da akakai yayi sanadiyyar ran wani yaro
- Sun kori sarkin tare da ahalinsa daga cikin garin
- Anyi kokarin jin tabakin sarkin amma ba'a sameshi ba

Asali: Facebook
Jama'ar dake zaune a yankin Ilogbo Ekiti a Ido Osi karamar hukumar jahar Ekiti sun kori sarkin su da iyalansa gaba daya daga cikin garin.
Yan garin sun bayyana cewa sarkin yana bada goyan baya wajen aikata barna a yankin,sannan ana lalata kayayyakin al'unmar yankin
DUBA WANNAN: IMN zasu fara tattaki zuwa Zariya
Da yawa daga cikin mutanen sunce ana yawan kawo musu farmaki tare da sanya hannun dan sarkin garin Adeleye Ajayi.
A wani hari da suka kaine sukayi sanadiyyar rasa ran wani yaro a cikin yankin.
Yan garin sun sanarwa da sarkin akan barnar da dansa yakeyi musu amma yayi burus da lamarin.
An samu nasarar kama dan sarkin tare da wasu mutane Bakwai,yayin da akakai gawar yaron mutuware .
Munyi kokarin jin tabakin sarkin amma hakan bai samu ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng