Yi wa doka da tsarin mulki hawan ƙawara ya fi sata barna – Symington

Yi wa doka da tsarin mulki hawan ƙawara ya fi sata barna – Symington

Mun samu labari daga Jaridun kasar nan cewa babban Jakadan Ƙasar Amurka a Najeriya ya bayyana babban abin da ya fi zama hadari a Najeriya kuma yace ba cin hanci ko kuma karbar rashawa bane.

Yi wa doka da tsarin mulki hawan ƙawara ya fi sata barna – Symington
Jakadan Amurka yace rashin adalci ya fi satar dukiyar jama’a illa
Asali: Depositphotos

William Stuart Symington wanda shi yake wakiltar Ƙasar Amurka a nan Najeriya yace watsi da dokar ƙasa da rashin adalci ya fi satar dukiyar al’umma zama hadari. Jakadan ya bayyana wannan ne a makon nan a Garin Ilorin.

Mista William Stuart Symington yayi jawabi game da tattalin arziki da kuma mulki a wajen yaye Dalibai a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara inda yace abin da yake dauka barna shi ne rashin adalci ba wai satar dukiyar Gwamnati ba.

KU KARANTA: Sojojin Kasan Najeriya sun kera wasu motocin yaki da hannun su

Har wa yau, Jakadan na Amurka yace idan har ana so Najeriya ta zama kamar Amurka, dole a samu kishin kasa da son gaskiya da adalci a ko ina aka sa gaba. Jakadan yace fatali da doka da rashin bin gaskiya babban matsala ne.

A jawabin da babban Jami’in na Ƙasar Amurka ya gabatar ya nuna alaƙar da ake da ita tsakanin tattalin arziƙi da kuma mulki mai nagarta. Yanzu Gwamnatin Shugaba Buhari dai tana kokarin dawo da gaskiya da yaƙar barna a Najeriya.

William Symington ya kuma nemi al’umma su tashi tsaye su rage dogaro ga Gwamnatin Kasar inda ya kuma yi kira a ajiye kabilanci da duk wani banbamci a gefe guda a rungumi ciyar da Najeriya gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng