Buratai zai kaddamar da wasu motocin da Sojojin Najeriya su ka kera a Zaria Ranar Asabar
Mun samu labari daga gidan Rediyon Rundunar Sojojin Najeriya cewa wasu dakarun Kasar sun kera wasu motoci na musamman na fita yaki da hannun su a kokarin da su ka yi na kara kwarewa wajen aiki.

Asali: Facebook
Yanzu dai mun samu labari cewa za a kaddamar da wadannan motocin da Sojojin Najeriya su ka kera a karshen makon nan. Shugaban Hafsun Sojin kasa Laftanan Janar Tukur Yusuf Buratai shi ne zai kaddamar da wadannan tan-tan.
Su kan su dai motocin an saka masu sunan Janar Tukur Buratai ne wanda shi ne Shugaban Rundunar Soji na kasa baki daya. An kera wadannan motoci na fita filin daga ne a gidan kananan Rundunar Sojoji na DEPOT da ke cikin Garin Zaria.
KU KARANTA: An zargi wasu gwamnonin APC 4 da shiryawa Buhari gadar zare
Wannan shiri dai yana cikin yunkurin da Manjo Janar VO Ezugwu wanda shi ne Shugaban gidan Rundunar kananan Sojin na Zaria yake yi na kara kwarewar Jami’an sa tare da hadin gwiwar Jami’ar ABU da kuma wata Hukumar kasa.
Samfurin motocin na farko yana iya daukar Sojoji 8 kuma ana iya canzawa motar fasali domin a gyara taku idan ana cikin filin daga. Sunan wadannan motoci TYB (Watau Tukur Yusuf Buratai) Rovers.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng