Kafin Kashoggi ya bata, ga wadanda suma Saudiyya ta batar, don suna sukar mulukiyyarsu

Kafin Kashoggi ya bata, ga wadanda suma Saudiyya ta batar, don suna sukar mulukiyyarsu

- An gano yadda kasar Saudiyya ke batar da masu caccakarta koda sun bar kasar

- Kasar ta Saudiyya na da kudin mai, shine dalilin da yasa ba'a iya tanka musu

- A baya, mata da maza sun bata, wadansu ma 'ya'yan sarakunan masarautar ne

Kafin Kashoggi ya bata, ga wadanda suma Saudiyya ta batar, don suna sukar mulukiyyarsu
Kafin Kashoggi ya bata, ga wadanda suma Saudiyya ta batar, don suna sukar mulukiyyarsu
Asali: Depositphotos

Ko da yake, duniya yanzu ta tabbatar da kisan gilla da aka yi wa dan jaridar Saudiyya mai gudun hijira, watau Khasshoggi, wanda ya bata daga shiga ofishin jakadancin kasar Saudiya a Turkiyya, wanda kuma yanzu aka tabbatar ya rasu, sai yanzu duniya ke waigen wadanda suma irin haka ya sanya ake zargin kashe su aka yi ko sacewa.

Kafin Kashoggi ya bata, ga wadanda suma Saudiyya ta batar, don suna sukar mulukiyyarsu
Kafin Kashoggi ya bata, ga wadanda suma Saudiyya ta batar, don suna sukar mulukiyyarsu
Asali: Getty Images

An fi zargin Muhamad bin Salman da irin wannan danyen aiki, saurayi mai jiran gado, wanda kuma ke ta tu'annati don yakar shia a kasar Yemen, da bama-bamai daga kasashen Turai.

DUBA WANNAN: Siysar Yanki: Abubuwan da Kwankwaso zai iya koya daga Tinubu

Ga kadan daga cikin wadanda suma suka yi wa kasar ta Saudiyya tawaye, suka tsere suke kuma tona ta, kuma suka bata ba amo babu labari, cikinsu kuwa, harda manyan 'ya'yan tsofin Sarakunan da suka mulki kasar.

Kafin Kashoggi ya bata, ga wadanda suma Saudiyya ta batar, don suna sukar mulukiyyarsu
Kafin Kashoggi ya bata, ga wadanda suma Saudiyya ta batar, don suna sukar mulukiyyarsu
Asali: Facebook

1. Yariman Saudiyya, Khalid bin Farhan ya bata a Jamus.

2. 'Yan mata hudu gimbiyoyi 'ya'yan tsohon Sarki Abdalla marigayi, sun bata tun zamanin mulkinsa, saboda sunyi karatu a Turai, sun bijirewa addini da al'adar kasar, sun sha yin bidiyo don duniya ta cece su, amma suna kulle a wani gida a Jidda ba aure babu sakata.

Kafin Kashoggi ya bata, ga wadanda suma Saudiyya ta batar, don suna sukar mulukiyyarsu
Kafin Kashoggi ya bata, ga wadanda suma Saudiyya ta batar, don suna sukar mulukiyyarsu
Asali: Facebook

3. Sultan bin Turki bin Abdulaziz

4. Saud bin Saif al-Nasr (An kashe shi a Saudiyyar bayan sato shi).

5. Yarima Turki al-Faisal bin Bandar (shima an kashe shi a Saudiyya)

Yanzu dai bayanan sirri sun tabbatar an kashe akalla biyu daga cikin wadannan bijirarru.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng